Daily Trust Aminiya - Mataimakin Gwaman Anambra ya koma APC

Mataimakin Gwaman Anambra ya koma APC

Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra, Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, har Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya karbi bakuncinsa.

Sauya shekar mataimakin gwamnan na Anambra daga jam’iyyar APGA zuwa APC na zuwa ne kimanin mako biyar kafin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba.

A ranar Laraba, Shugaban Rikon Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya jagoranci Mista Okeke zuwa Fadar Shugaban Kasa domin ganawa da Buhari.

Sun kuma samu rakiyar Gwamnan Jihar Imo, Sanat Hope Uzodinma, wanda shi ma dan jam’iyyar APC ne, a ziyarar da suka kai wa Buhari.

Karin larabi na tafe.

Karin Labarai