✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakin gwamnan Zamfara ya ki bayyana gaban kwamitin da ke bincikarsa

Kwamitin ya ce zai tabbatar da adalci a yayin gudanar da bincike.

Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, ya ki bayyana gaban kwamitin da aka kirkira don gudanar da bincike a kansa kan zargin almundahana da dukiyar gwamnati.

Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), ya rawaito cewar kwamitin na mutum bakwai, wanda mai shari’a Halidu Tanko ke jagoranta, ya fara zaman bincike kan badakalar da ake tuhumar Mahdi Aliyu a Babbar Kotun jihar da ke Gusau a ranar Litinin.

Sai dai mataimakin gwamnan bai halarci zaman kwamitin ba a ranar Talata, sannan lauyansa ma bai bayyana a gaban kwamitin ba.

Da ya ke jawabi, Tanko ya jinjina wa jama’ar jihar yadda suka bai wa kwamitin hadin kai wajen gudanar da zaman da suka yi na kwana biyu.

Kazalika, da ya ke magana, mai shari’a Abdul Ibrahim (SAN), daya daga cikin mambobin kwamitin, ya ce za su tabbatar da adalci yayin gudanar da binciken nasu.

“Aikinmu zai kasance kan doron kundin tsarin mulki, mun bai wa kowane bangare damar gabatar da hujojjinsa.

“Za mu gabatar da bincikenmu yadda ya kamata, saboda wata uku kacal gare mu.

“Za mu duba komai cikin tsanaki, da zarar komai ya kammala za mu gabatar da shi gaban majalisa,” in ji shi.

A cewarsa, rashin bayyanar mataimakin gwamnan gaban kwamitin ba zai shafe binciken da su ke gudanarwa ba, “don aikinmu shi ne bai wa kowane bangare dama, kuma mun bayar da damar tun kafin fara zamanmu.

“Duk wani bangare da ya ki bayyana a gaban kwamiti ba abin da ya shafe mu ba ne,” a cewarsa.

Tun a ranar 9 ga watan Fabrairu ne Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta umarci  alkaliyar alkalan jihar, Kulu Aliyu da ta kafa kwamitin da zai binciki mataimakin gwamnan kan zargin da ake masa na yin almundahana da wasu kudaden da su ka shafi ofishinsa.

Sai dai mataimakin gwamnan Jihar Mahdi Aliyu Gusau, ya bayyana cewar ana masa makarkashiya ce saboda ya ki hada sahu da gwamnan Jihar, Muhammad Bello Matawalle wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.