✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mataimakin shugaban Karamar Hukuma ya mutu a Kano

Kafin rasuwarsa, shi ne Mataimakin shugaban Karamar Hukumar Ungogo.

Mataimakin shugaban Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Dantalata Karo ya rasu.

Shugaban Karamar Hukumar, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

Ya ce, “Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un. Allah ya jikan Alhaji Abdullahi Dantalata Karo (Mataimakain Shugaban Karamar Hukumar Ungogo). Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashinsa, mu kuma ya sa mu yi kyakkyawan karshe.”

To sai dai sanarwar ba ta fadi musabbabin rasuwar tasa ba.

Rahotanni dai sun ce za a gudanar da jana’izarsa ranar Litinin a Kano.

Kafin rasuwarsa, marigayin shine ke rike da mukamin Mataimakin shugaban Karamar Hukumar ta Ungogo, kuma ya taba zama shugaban jam’iyyar APC mai mulki na yankin Karamar Hukumar .

Ya kuma taba tsayawa takarar shugabancin Karamar Hukumar, kafin daga bisani a yi maslaha ya tsaya a matsayin mataimaki.