✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai ya sake lashe kujerarsa a Filato

Ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP inda ya yi nasarar

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, na jam’iyyar APC, ya sake lashe kujerar ta mazabar Wase da ke Jihar Filato.

Jami’in zabe na yankin, Farfesa Sati Umaru Fwatshakya ne ya bayyana sakamakon.

Ya cewa Ahmed Wase ya sami kuri’a 31,499.

Kazalika, abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Ibrahim Bawa Kanji ya sami kuri’a 25,513 a zaben.