✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan nada Khalifan Tijjaniyya — Sheikh Dahiru

Akwai matakai uku da ake bi wajen nada Halifan Darikar Tijjaniyya.

Sanannen Malamin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce akwai matakai uku da ake bi wajen nada Halifan Darikar Tijjaniyya.

Shehin ya bayyana hakan bayan da ya tarbi Sarkin Kano kuma Khalifan Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi na II ranar Litinin a gidansa da ke Bauchi.

A cewar Shehin, akwai wanda Sheikh Ibrahim Nyass yake nada wa da kansa, sai kuma idan shi wannan Khalifan ya mutu, dansa yakan gaje shi, sannan akwai wanda Shehunnan darikar ke nadawa domin samun jagora cikin al’umma masu yawa idan ba su da jagora.

Nadin Sarki Muhammadu Sanusi ya fada a mataki na uku a cewar Shehun na Bauchi.

Tun da farko, kafin ya gabatar da jawabinsa, Shehin ya bukaci da a karanta masa takardar da shi sabon Khalifan, Muhammadu Sanusi, ya zo da ita daga Kaulaha.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa bayan da aka karanta takardar, a cikin jawabinsa ya ce: “Ina taya ka (Sarki Muhammadu Sanusi II) murna, na samun wannan takarda da wannan mukami na Khalifanci.

“Kuma muna maraba da wannan Babban Bako wanda nan gidansu…,” inji Shehin.

A cewarsa, asalin Khalifanci Sheikh Ibrahim Inyass ya bai wa Sarkin Kano Sanusi na I ya faru ne bayan an cire Sarkin daga sarauta.

“Wata rana mun je Makka, sai Shehu Ibrahim yana tambaya na labarin Najeriya ina ba shi har muka iso kan labarin Khalifa Muhammadu Sanusi I.

“Na ce masa an sauke shi daga sarautar Kano inda ya koma Azare… Sai Shehu ya ce tunda mutanen duniya sun raba shi da jama’a, sai Shehu ya hada shi da mutanensa.

“Ya aike ni na je na fadawa mukaddaman Kano musamman Shehu Tijjani.

“Na tara Shehunan Kano na fada musu cewa Shehu ya nada mana Khalifa bayan na fadawa Shehu Tijjani da sauransu.

“Da shekara ta kewayo Shehu ya aiko da takarda a rubuce ta nadin,” inji Shehu Dahiru.