✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla

Bayani dalla-dalla kan matakan soyayya da yadda ake dabbaka su a rayuwar aure.

Soyayyar na da matakai da suke faruwa daya bayan daya a tsawon lokacin gudanarta, kuma matakin farko shi ke haifar da na biyu, na biyu ya haifar da na uku, haka dai har zuwa ga cikarta da kammaluwarta.

Wannan shin abin da za mu mayar da hankali a kai a ci gaban bayani da muke yi kan ilimin soyayya domin ma’aurata su fahimci wannan babban jigo na rayuwar aure kuma su dabbaka soyayya cikin huldodinsu da zamantakewar aurensu.

Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili na Don Ma’aurata, inda a wannan karon za mu yi bayani a kan Matakan Soyayyar Auratayya.

Soyayyar auratayya tana da matakai guda hudu:

  1. Magagin kauna
  2. Farkawa daga magagin kauna
  3. An zama daya
  4. Kammaluwar soyayya

 Magagin kauna

Shi ne farkon aure, lokacin ana cikin ganiyar so da kauna da sha’awar juna.

Sai dai wannan magagi zai rika sakin su kadan-kadan har wata rana su wayi gari su nemi wannan magagin kauna su rasa.

Shi dama magagin kauna wasu sinadaran rai ne (hormone odytocin) ke sihirce zuciya da shaukin jin dadi da ma’aurata kan ji a wannan lokaci, musamman don su tabbatar da kuma saukake faruwar ibadar aure tsakanin ma’aurata.

Da hakan ya faru kuwa, sun kammala aikinsu, sai su janye su koma bangaren sanya soyayya tsakanin iyaye da dan da suka haifa.

Don haka sai ma’aurata su dage wajen ginawa da shuka abubuwan alfanu yayin da suke cikin magagin kauna, domin yin hakan zai saukaka rikirkicewar da farkawa daga magagin kauna ke haifarwa.

  1. Farkawa daga magagin kauna

Wannan mataki ne mai rikirkita rayuwar aure da bice soyayya nan da nan daga zuciyar ma’aurata.

Bayan farkawar ma’aurata daga magagin kauna, za su ga abubuwa da yawa na tare da junansu da irin shaukin jin dadin da suke ji game da juna duk sun canja.

Kokarin da suke yi wajen faranta ran juna, yanzu ko rabinsa ba su iyawa, abubuwan da yawa da suke sharewa a matakin farko, yanzu sai ya kasance abin da bai kai ya kawo ba ya sa sun yin jayayya da ka-ce-na-ce; abuwawan da ya sa suke burge juna a da, yanzu haushi yake ba su.

Don haka a hankali sai magudanar soyayyarsu ta tsaya cak ba ta gudana.

Kuskuren da ma’aurata kan yi bayan sun farko daga magagin kauna, shi ne na kasa fahimtar cewa magagin kauna ba shi ne kadai kaunar da ke tsakaninsu ba, akwai ingantacciya kuma sahihiyar soyayyar da Allah Yake sanyawa a cikin zuciyar dukkan ma’aurata.

Tunda sun daina jin fisgar magagin kaunar da sukan ji a matakin farko, to ai shi ke nan soyayya ta kare, sai dai a yi zaman hakuri ko zaman ’ya’ya!

Wadanda kuma suka kasa yin hakurin, sai abin ya kai su ga mutuwar aure.

To mu sani Allah bai hukunta aure don a yi zaman hakuri ko zaman ’ya’ya ba.

Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) Ya hukunta aure ne domin a natsu da juna kuma a zama tufar suturce juna.

Ma’auratan da ke cikin wannan mataki sai su yi kokarin gina sahihiyar soyayyarsu ta asali su mance da wancan magagin kaunar na matakin farko domin samun aminci da natsuwa cikin rayuwar aurensu.

  1. An zama daya

Wannan mataki yana tattare da kammaluwar amintaka da fahimtar juna a tsakanin ma’aurata; yanzu ma’aurata da wuya a ji suna ka-ce-na-ce ko jayayya, suna tsananin hakuri da juna da mutunta juna a wannan mataki, kuma suna kokarin kare dukkan hakkokin juna; ma’aurata ba su hantarar juna ko jin kyashin juna ko raini.

A irin wannan matakin za ka ji uwargida na tsananin daraja mijinta da girmama shi kamar dai shi wani magabacinta ne ba mijinta ba.

Maigida kuma ka ga bai son a fadi laifin matarsa bai kuma son abin da zai bata mata rai.

  1. Kammaluwar soyayya

Shakuwa da sabo da juna da gwagwarmayar da ma’aurata suka sha a matakai ukun farko, sun hadu sun gina wata irin soyayya ta musamman tsakaninsu; suna jin dadin juna kuma ba su fatar rabuwa da juna.

Ko matsala ta fado musu cikin rayuwar aurensu, tare za su fuskance ta su magance ta domin sun zama daya a ruhi da kuma a sarari.

Karin bayani:

Wadannan matakai sun bambanta tsakanin ma’aurata bisa ga yanayi da silar da ta kulla auratayya tun asali:

  • Yawanci ma’aurata magagin kauna ne ke zama sanadin kulluwar auratayyarsu, sai dai wannan magagin kauna bai da tsawon rai cikin rayuwar aure, nan da nan zai saki ma’aurata su farka.

Wannan farkawa ce za ta shigar da su zuwa ga mataki na biyu.

  • Wadansu ma’auratan kuwa na fara rayuwar aurensu, ba so da kauna, ba yarda ba amincewa; ko daya na so daya bai so ko daya ya amince, dayan bai amince ba.

Misali kamar ma’auratan da aka yi wa auren dole ta bangare daya ko ta duka bangarorin.

To a irin wadannan ma’aurata, idan suka samu fahimtar juna a tsakaninsu, ta iya yiwuwa su tsinci kansu tsundum cikin magagin kauna, wato matakin farko ke nan, kafin daga baya su farka ko kuma soyayyarsu ta tafi a hankali, suna kara shakuwa da juna soyayya da kaunarsu na kara zurfi, wato za su fara a mataki na uku ke nan.

  • Wadansu ma’auratan yarda da amincewarsu ga juna ne abin da ya yi silar kulluwar aure tsakaninsu.

Don haka za su fara rayuwar aurensu ba tare da magagin soyayya mai makantar da hankali ba.

Irin wadannan ma’aurata sukan fara aurensu ne ba romansiyya cikin soyayyarsu, amma suna kara shakuwa, soyayyarsu na kara ginuwa, su ne ma’auratan da kan fara rayuwar aurensu a mataki na hudu.

  • Akan samu ’yan kadan daga cikin ma’aurata da magagin kaunarsu bai bacewa a duk tsawon auratayyarsu.
  • Wadansu ma’auratan kuwa mataki na biyu za su kare auratayyarsu, su kasa samun kwarewar da za ta shigar da su mataki na uku.
  • Wata matsalar na iya fadowa cikin ma’auratan da suke mataki na uku har ta yi illar maida su matakin rikici, wato mataki na biyu.
  • Wadansu ma’auratan kuwa a mataki na ukun nan suke kare rayuwarsu ba tare da sun kai ga na hudu ba.

Sai mako na gaba in Allah Ya yarda.