✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakin G7 na karya farashin man Rasha ya fara aiki

Duk wata biyu za a sauya farashin domin tabbatar da danyen man Rasha ya yi kasa da akalla kashi 5 cikin 100 na farashin OPEC

Takunkumin da manyan kasashen duniya (G7) suka sanya na karya farashin danyen man da Rasha ke fitarwa ta teku zuwa Dala 60 ya fara aiki.

Kasashen G7 da Australiya da kasashe 27 na  Tarayyar Turai (EU) sun sanya mizanin farashin da ya fara aiki a ranar Litinin ne da nufin hana Rasha samun kudaden daukar nauyin yakinta da Ukraine.

Sun kuma haramta wa kamfanoni masu zaman kansu bai wa Rasha tankokin daukar mai, idan ba za ta sayar da danyen man nata a Dala 60 ko kasa da haka ba.

Haka kuma an haramta ba su taimakon kudi ko wata hidima, idan farashin ya haura haka, idan ba a lokacin ibtila’i ko tsautsayi ba.

Duk jirgin wata kasa da ya dauki man Rasha a fiye da Dala 60 kuma za a haramta masa inshora da graya da samun kudade na tsawon kwana 90.

A cewarsu, hakan zai samar da daidaito a kasuwar danyen mai ta duniya tare da ba wa wasu kasashe damar sayen man Rasha da ke kan teku, idan farashinsa ya kai ko ya gaza Dala 60 da suka kayyade.

Bayan duk wata biyu za a sauya farashin, farawa daga tsakiyar watan Janairun 2023, domin tabbatar da farashin man Rasha ya yi kasa da akalla kashi 5 cikin 100 na farashin da Kungiyar Kasashe Masu Hako Mai ta Duniya (OPEC) ta kayyade.

Duk sauyin da za a yi sai ya samun amincewar daukacin kasashen EU 27 da Australiya da kuma kasashen G7.

Duk lokacin da aka kayyade farashi zai samu sassaucin kwana 90 domin tabbatar da cewa bai shafi jiragen ruwan da ke dauke da mai a kan teku kafin a yi karin ba.