✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matan Hausawa suka yi watsi da al’adun al’ummarsu

Riko da al’adun mutanen Yamma da matan Hausawa ke yi ya yi tasiri a kowane fanni na rayuwarsu.

Masana na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda ake samun karbuwa na al’adun mutanen Yamma wato Turawa wanda hakan yake kore al’adu da dabi’un da aka sani a kasar Hausa.

An bijiro da wannan maudu’i ne yayin taron kasa kan mata da kuma gudunmuwar da suke bayarwa a cikin al’ummar Hausa wanda sashen nazarin harsunan Afirka na Jami’ar Al-qalam tare da hadin gwiwar Kwalejin Ci gaba da Karatu ta Pleasant a Jihar Katsina suka dauki nauyi.

Aminiya ta ruwaito cewa, an gudanar da taron kan makala mai taken ‘Kalubale da Gudunmuwar  da Mata ke bayarwa wajen ci gaban al’ummar Hausawa tun daga mafarar lokaci har zuwa karni na 21.’

A jawabinta na musamman da a gabatar ranar Litinin a Katsina, Shugabar Kwalejin, Dokta Yusuf Bala da Daura, Farfesa Sadiya Sani Daura, ta bayyana damuwa kan yadda matan Arewa ke dabi’antuwa da al’adun Turawa.

A cewarta, riko da al’adun mutanen Yamma da matan Hausawa ke yi ya yi matukar tasiri a kowane fanni na rayuwarsu, lamarin da ta ce akwai bukatar su rika tunawa da illar hakan.

Farfesa Sadiya ta ce mata a kasar Hausa sun yi watsi da ainihin al’adunsu na salon sanya tufafi, rubuce-rubuce, girke-girke na abincin gargajiya da sauran ababen da suka shafi al’adunsu na asali.

“Galibinmu ba mu san abin da ke faruwa ba, amma ina fatan a karshen wannan taro, mahalartansa za su tsinci wasu muhimman ababe da za su koma gida da su domin kawo mafitar da za ta magance wannan matsala da muke neman dulmiyewa a cikinta.

“Hausawa sun kasance daya daga cikin manyan kabilu a Yammacin Afirka, amma sun fi yawa a Najeriya, Jamhuriyyar Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Togo, Burkina Faso da Jamhuriyyar Benin.

“Harshen Hausa yana kunshe da dogayen kalmomi da dama musamman wadanda aka aro daga harshen Larabawa kasancewarsa shi ne yaren babban addini a kasar Hausa, wato musulunci.

“Kamar yadda addini yake da wani bigire na musamman a kan Hausawa, haka ma al’ada tana taka muhimmiyar rawar gani a rayuwarsu.

“A wurinsu, addini da al’ada su ne muhimman ababen da ke tasiri a fannin da yanayi na jinsin mutum yake da ruwa da tsaki, wanda wannan shi ya bude kofar da ake bukatar a dama da mata su bayar da gudunmuwa domin ci gaban al’umma,” a cewarta.

A nasa jawaban, Mataimakin Shugaban Jami’ar Al-qalam, Farfesa Muhammad Abubakar, yay aba wa wadanda suka shirya taron musamman kuma da suka zabi tattaunawa a kan wannan maudu’i.

Y ace taron ya zo a kan gaba a daidai lokacin da mata suka fi mayar da hankali wajen daukar dabi’u irin na mutanen Yamma da sauran munanan al’adu da ba su san sub a.

Ya kuma yi kira ga matan Arewa musamman Hausawa da su yi watsi da irin wadannan al’adu su rungumi nasu al’adun na asali da kuma addini domin samar da al’umma ta gari.

Farfesa Abubakar ya kuma bayyana fatan cewa taron zai taimaka wajen farfado da al’adun gargajiya musamman ma na matan Hausawa.