✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Borno sun bukaci jami’an tsaro su sauya salon yakar ’yan ta’adda

Kungiyoyin matan sun bukaci hukumomin tsaro su ba wa mata da kananan yara kariya ta musamman

Gamayyar kungiyoyin mata a Jihar Borno, sun koka kan mawuyacin hali da mata da kananan yara suka shiga sakamakon harin baya-bayan nan a yankunan Damasak da Dikwa.

Kungiyoyin matan sun kuma bukaci hukumomin tsaro da su sauya salonsu na yaki da ’yan ta’adda.

Shugabar gamayyar Kungiyoyin, Fatima-Askira Satomi ta shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa lallai suna bukatar a samar da wasu dabarun kare mata daga harin ’yan ta’adda.

“Damuwarmu ita ce yanayin da mata suka tsinci kansu na matsanancin hali a garuruwan Damasak da Dikwa; Lallai abun yana da tsananin tayar da hankali, kuma muna bukatar kulawa.

“Muna kira da babbar murya ga Sojoji da su kara ba wa mata da kananan yara kariya da kulawar da ta kamace su musanman a irin wannan yanayin.

“Na kama sunan mata da jami’an tsaro ne a kiraye-kirayena saboda yana da matukar muhimmanci, yana da kyau a ba wa mata da yara kulawa ta musanman a ire-iren wadannan wurare da a baya-bayan nan ’yan ta’adda suka kai hari.

“Ina nufin yankin Damasak da Dikwa, Ina tunanin ya kamata mu sauya sabon salo na tunkarar ’yan ta’adda da bullo da dabarun bawa mata da yara kariya.

“Ina nufin a ba wa mata da yara kariya ne ta bangaren garkuwa da fyade  da cewa lallai a sanya ido da kuma daukar matakan kariya,” a cewar Fatima.