✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Matan da suke fitar da kanshi daga jikinsu

Ta ce a lokacin al’adarta, kamshin yana raguwa da kusan kashi 10 cikin 100.

Yayin da mafi yawan jama’a suke amfani da turare ko nau’o’in wasu man kula da gyaran fata, an samu wadansu mata a kasar Vietnam da aka ce suna fitar da kanshin fure daga halittar jikinsu.

Daya daga cikin matan mai suna Dang Thi Tuoi, mai sana’ar dinki daga Lardin Sóc Trăng na kasar Bietnam, an ce tana da baiwa mai ban mamaki sosai.

Idan aka shafa fatarta tana fitar da wannan kanshi mai dadi, irin na fure wanda za a iya kwatanta shi da turare.

An bayar da rahoton cewa, Dang tana da wata baiwa ta musamman a jikinta a shekaru da suka gabata, yayin da idan ta shafa hannuwanta da kafafunta bayan ta yi aiki a yini, nan take sai ta ji kanshi mai dadi a karshe ta gano kanshin yana fitowa ne daga jikinta.

“A yini idan ina son jin kanshin, sai in shafa jikina in mutsuttsuka hannuwana, amma da daddare makwabtana suna jin kanshin da ke fitowa daga jikina ko da akwai nisan mita tsakanina da su,” Dang ta shaida wa tashar YouTube ta Doc La Binh Tuong.

Dang, ta yi ikirarin cewa wasu wurare a jikinta sun fi sauran fitar da kanshin, kuma kanshin ya fi karfi da daddare fiye da na rana.

Ta ce a lokacin al’adarta, kamshin yana raguwa da kusan kashi 10 cikin 100, amma yana da karfi idan aka cika wata, ko a ranar farko ta wata.

Labari mai ban-mamaki game da Misis Tuoi ya dauki hankali sosai a kafofin labarai na zamani, tare da ainihin bidiyon da aka wallafa a kafar YouTube, inda ya samu masu sharhi sama da miliyan 1.7 bayan sun kalli bidiyon.

Mutane sun yi mamakin irin karfin da matar take da shi.

Bayan nasarar wallafa faifan bidiyo na farko a tashar Doc La Binh Tuong, inda wata mata ta tuntubi wacce ta yi ikirarin cewa tana da nata turaren.

Sai matar ta biyu mai suna Dung, wacce ’yar asalin Lardin Kien Giang, ta yi ikirarin cewa kamar yadda Dang Thi Tuoi, jikinta ke fitar da kanshi mai dadi idan an shafa shi, ta dade da sanin wannan halitta ta musamman, domin duk lokacin da ita ma ta shafa hannuwanta a fatarta sai ta ji wani kanshi mai karfi, amma ba ta taba gaya wa kowa ba.

Babu daya daga cikin matan biyu da suka bayyana dalilin da ya sa jikinsu ke fitar da irin wannan kanshi kamar turare.