✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata sun yi zanga-zanga a Kaduna kan sakamakon zaben gwamna

Matan sun yi zanga-zangar ne kan nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan Jihar.

Wasu mata a Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu kan ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Matan sun kuma bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta sake duba sakamakon zaben da aka gudanar.

Aminiya ta ruwaito cewa matan da suka yi zanga-zangar, sun mamaye ginin Majalisar Dokokin Jihar  sanye da bakaken kaya dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce.

Idan dai za a iya tunawa, jami’in zaben Jihar Kaduna, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, ya bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 730,002 yayin da Isah Ashiru na PDP ya samu kuri’u 719,196.

Sai dai da ta ke zantawa da manema labarai a ranar Talata, wata tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma, Kwamared Aishatu Madina, ta zargi jam’iyya mai mulki tare da hadin gwiwar Hukumar Zabe da rashin bin doka.

A cewarta, “Sakamakon zaben ya nuna cewa PDP ce ta lashe zaben duk da kokarin da aka yi na soke sakamakon zaben.

“Yawan kuri’un da aka soke sakamakon zaben ya zarce tazarar da INEC ta yi amfani da ita wajen ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben.”

Ta kara da cewa sakamakon da aka bayyana bai nuna zabin da akasarin mutanen Jihar suka yi ba.