✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Abdulmalik Tanko ta nemi ya sake ta kara aure, bayan kotu ta wanke ta

Jamila ta ce ba za ta iya jiran Abdulmalik Tanko ba

Jamila Muhammad Sani, matar malamin nan da ake zargi da kashe dalibarsa Hanifa a Kano, wato Abdulmalik Tanko, ta bukaci ya sake ta je ta yi wani auren, domin ba za ta iya jiran shi ba.

Jamila ta yi wannan bayani ne jim kadan bayan kotun ta wanke ta daga zargin hada baki da mijinta, Abdulmalik Tanko, wajen sacewa da kuma kashe Hanifa Abubakar.

“Ni da har yanzu ina da sauran kuruciyata. Ba zan iya zaman jiran shi ba. Ina neman ya sake ni kawai in je in samu wani mijin in aura. Ni ba zan iya zaman jiransa ba,” inji ta.

Da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan wanke ta da kotun ta yi, Jamila mai shekara 30 ta gode wa Allah bisa wanke ta da aka yi daga zargin tana da hannu a lamarin, inda ta ce ta dan samu sauki a zuciyarta.

Abdulmalik ya yi ikirarin kasha Hanifa

A ci gaba da sauraron shari’ar a ranar Laraba, kotun ta bayyana cewa babu wanda ya tursasa Abdulmalik Tanko ya yi ikirari a gaban kotun cewa shi ya kashe dalibarsa Hanifa da kuma yadda ya kashe ta.

Kotun ta yanke wannan huknuci ne bayan a makon jiya ne Abdulmalik ya musanta kashe Hanifa, inda ya ce an tursasa shi ne ya yi wannan jawabi.

Abdulmalik ya yi mi’ara-koma-baya ne bayan Kotun Majistare din Mai Lamba 12 da ke Gidan Murtala a birnin Kano ta wanke tare da sallamar matarsa Jamila.

Hukuncin kotun na makon jiya ya biyo bayan gamsuwa da shaidar da ta bayar a gaban kotun, inda kotun ta gano ba ta da hannu a cikin lamarin.

Kotun, a karkashin Mai shari’a Muhammad Jibril ta wanke Jamila a kan zargin da ake yi mata na boye Hanifa.

Tun da farko dai lauyan gwamnati, Barista Lamido Soron-Dinki, ne ya gabatar da karar, kuma kotun ta yi la’akari da bayanan da Jamila ta bayar tare da yin nazari inda ta gano ba ta da laifi a kan batun sace Hanifa Abubakar da kuma kashe ta.

Abin da na sani game da kisan Hanifa —Jamila

Da take bayani kan lamarin, Jamila ta zayyana wa kotun duk abin da ta sani game da kamawa, tsarewa da kuma kisan Hanifa.

Jamila ta amsa tambayoyi daga lauya mai gabatar da kara, Barista Musa Lawan, inda ta yi wa kotu bayani kan abin da ta sani game da zargin dauke Hanifa, wacce daliba ce a makarantar mallakin mijinta Abdulmalik.

Ta ce ya kawo mata yarinya, ta tambaye shi ina iyayenta, sai ya ce da ita uwar yarinyar malama ce a makarantar amma ta samu aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don cike wasu takardu.

“Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba, sai nake tambayar shi yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?

“Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar,” inji Jamila.

Ta ci gaba da bayyana wa kotun cewa bayan kwana biyu sai ya sake ce mata uwar yarinyar ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayar shi, sai ya ce ta daina tambayarsa.

Matar Abdulmalik ta ce ta kai ga sanin sunan yarinyar ce a tsawon kwanakin farko da kai Hanifa gidan, a lokacin da take kuka, ita kuma ta rarrashe ta ta hada ta da ’ya’yanta biyu don yin wasa wanda hakan ya debe mata kewa.

Ta shaida wa kotun cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa lakabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.

Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijinta Abdulmalik magana ya ce kudin mahaifiyar yarinyar ne ya kare tana Kaduna. Amma saboda yadda ta matsa masa, sai ya fada mata cewa zai mayar da Hanifa.

Jamila ta kara da cewa a daren rana ta 5 ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara barci, ya ce a dauko kayan makarantarta a sa mata. Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin karfe 11:00 na dare, amma haka ya tafi kai ta a cewarsa.

“Lokacin da ya dawo na fara barci, na kuma tambaye shi ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce ‘eh’.

 “Bayan ’yan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta, sai ya ce ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya sa masa a caji,” inji ta.

Ta ce Hashimu amininsa ne na kut-da-kut wanda ta san su tare tun kafin aurensu.

Lauyan Abdulmalik, Barista Muktar Labaran Kabo ya fara tambayar Jamila ko shin tana da rediyo da talabijin da take saurara? Sai Jamila ta amsa masa cewa tana ji.

Ya sake tambayarta duk tsawon lokacin da Hanifa ke gidanta, ba ta taba jin cewa ana neman wata yarinya, ko makwabta su fada mata ana neman wata yarinya ba?

Sai ta ce masa ba ta saurarar rediyo sai dare shi ma shirin Karkade Kunnuwa na Rahama kawai take saurara.

Ya kara tambayarta ko tana da makwabta kuma tana zuwa wajensu? Sai ta ce tana da su, amma ba ta zuwa gidajensu sai da kwakkwaran dalili.

A karshe lauyan ya tambaye ta, ta ina ta samu labarin an sace Hanifa, duk da ta ce ba ta sauraren rediyo, sai ta ce ba ta taba ji ba sai da ma’aikatan DSS suka gayyace ta.

Da wadannan bayanai aka kammala karbar shaidar Jamila.