✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Abdulmalik Tanko ta bayar da shaida a kansa

Na tambaye inda iyayenta suke sai ya ce uwar yarinyar malama ce a makarantarsa amma ta sami aiki a Saudiyya.

Jamila Muhammad Sani, matar Abdulmalik Tanko, mutumin da ake zargi da kisan Hanifa a Kano, ta bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis da safe.

Jamila ta tsaya a gaban Babbar Kotu da ke zamanta a Audu Bako karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na’abba a matsayin mai bayar da shaida kan tuhumar da ake yi wa mijinta da sace tare da kashe yarinyar ’yar shekara biyar a watan Janairu.

Jamila ta amsa tambayoyi daga lauya mai gabatar da kara, Barista Musa Lawan, inda ta yi wa kotu bayani kan abin da ta sani game da zargin dauke Hanifa, wacce daliba ce a makarantar da ta zama mallakin mijinta Abdulmalik.

Ta ce ya kawo mata yarinya ta tambaye shi ina iyayenta sai ya ce da ita uwar yarinyar malama ce a makarantsar amma ta sami aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don cike wasu takardu.

“Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba sai nake tambayarsa yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?

“Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar ba,” in ji Jamila.

Ta ci gaba da bayyana wa kotu cewa bayan kwana biyu sai ya sake ce wa mata uwar yarinyar ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayarsa, sai ya ce ta daina tambayarsa.

Matar Abdulmalik ta ce ta kai ga sanin sunan yarinyar ne a tsawon kwanakin farko da kai Hanifa gidan, a lokacin da take kuka, ita kuma ta rarrasheta ta hada ta da ’ya’yanta biyu don yin wasa wanda hakan ya debe mata kewa.

Ta shaida wa kotu cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa lakabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.

Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijin nata Abdulmalik magana ya ce kudin mahaifiyar yarinyar ne ya kare tana Kaduna.

Amma saboda yadda ta matsa masa, sai ya fada mata cewar zai mayar da Hanifa wajen babarta.

Jamila ta kara da cewa a daren ranar na 5 ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara bacci, ya ce a dauko kayan makarantarta a saka mata.

Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin 11 na dare, amma haka ya tafi kai ta a cewarsa.

“Lokacin da ya dawo na fara bacci, na kuma tambaye shi cewar ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce ‘eh’.

“Bayan ’yan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta sai ya ce min ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya saka masa caji,” kamar yadda ta bayyana.

Ta ce Hashimun amininsa ne na kut-da-kut wanda ta sansu tare tun kafin aurensu.

BBC ya ruwaito yadda lauyan Abdulmalik wanda da ake kara Barista Muktar Labaran Kabo ya fara tambayar Jamila ko shin tana da rediyo da talabijin da take saurara?

Sai Jamila ta amsa masa cewar tana ji.

Ya sake tambayarta duk tsawon lokacin da Hanifa ke gidanta, ba ta taba jin cewar ana neman wata yarinya, ko makota su fada mata ana neman wata yarinya ba?

Sai ta ce masa ba ta saurarar rediyo sai dare shi ma shirin Karkade Kunnuwa na Rahama kawai take saurara.

Ya tambayeta suna mahaifiyar yarinyar, sai ta ce Murjanatu sunanta.

Ya kara tambayarta ko tana da makota kuma tana zuwa wajensu? Sai ta ce tana da su, amma ba ta zuwa gidajensu sai da kwakkwaran dalili.

Sannan ta kara da cewa “tun ranar Asabar ya kawo ta gida har zuwa ranar Alhamis” wato kwana biyar kenan.

Lauya Muktar Labaran Kabo ya tambayi Jamila ko tana da yaro mai shekaratakwas ko hudu, kuma wacce makaranta yake zuwa?

Sai ta ce makarantar mai gidanta, wato inda Hanifa take kenan.

A karshe lauyan ya tambayeta, ta ina ta sami labarin an sace Hanifa, duk da ta ce ba ta sauraren rediyo, sai ta ce ba ta taba ji ba sai sanda DSS suka gayyace ta.

Da wadannan bayanai aka kammala karbar shaidar Jamila.

Alkalin ya dage sauraron karar zuwa 9 da kuma 10 ga watan Maris din da muke ciki.