✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar aure mai sana’ar tuka Keke NAPEP a Kano

'Sai Mama' ta ce babur dinta ya fi karfin maza, "nakan iya dage kafa daya yadda maza ke yi.''

Malama Amina Ibrahim Daneji, wacce ake wa lakabi da Sai Mama, matar aure ce mai ’ya’ya bakwai da ta zama kallabi tsakanin rawuna, duba da yadda ta shiga sahun masu sana’ar tukin babur mai kafa uku wanda aka fi sani da ‘A Daaidaita Sahu’ a Kano.

A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana yadda aka yi ta fara wannan sana’a da kuma irin burin da take da shi a kan sana’ar.

Yaya aka yi kika fara sana’ar tukin a daidaita sahu?

To ni dai zan iya cewa sha’awa ce, domin maigidana ya dade yana gudanar da wannan sana’a.

Yana daga cikin mutane na farko da gwamnati ta fara ba su irin wanann babur din a lokacin mulkin Malam Shekarau.

To tun wanann lokacin nake sha’awar tukin sai dai ban samu dama ba domin a wancan lokacin yakan kasance ko ina da ciki ko kuma ina goyo. Sai a yanzu na samu dama na fara.

Kasancewar ina sha’awa a duk lokacin da za mu fita da mai gidana ina mayar da hankalina a kan tukin da yake yi. Ina kallon abubuwan da yake yi.

Kai a wasu lokutan ma har tambayoyi nake yi masa game da wasu abubuwa da ban gane ba, shi kuma sai ya min bayani. Wasu lokutan sai ya tambaye ni to me ya sa nake so na sani ni kuma sai na ce haka kawai.

Ban fara tukin ba sai kimanin wata hudu da suka gabata, watarana ya dawo gida sai na ce masa ya je ya sayo min magani a kemis sai ya ce shi ya gaji ba zai fita ba.

Ni kuma sai na ce ya ba ni makullin babur din sai ya ba ni. Ya yi zaton wasa nake yi sai na sa hijabina na fita na je na tayar na tafi kemis din.

Yarana suka dawo gida da gudu suka gaya masa cewa na tayar da babur. Hakan ya sa ya fito da sauri ai kuwa sai ya tarar na tafi.

Da na je na gama sayen maganina na dawo gida sai na iske shi a kofar gida rigarsa a hannu ya yi tagumi.

Na zo na ajiye babur din kamar yadda na dauka. Na sauka na wuce gida abina na bar shi a waje yana mamaki.

Bayan kwana biyu sai na sake daukar babur din tun daga unguwarmu Sheka na tafi gidan kanwata a Dorayi. Tun daga nan sai hanya ta bude na fara hawa sosai.

To lokacin da na sanar da maigidana cewa zan rika hawa ina yin haya da shi sai muka yanke shawarar na je na yi rajista da kungiya.

Da na je ofishin Kungiyar TOKAN, shugaban kungiyar ya yi mamakin jin abin da na zo da shi inda ya nemi na tuka a gabansa.

Nan ya shiga na tuka shi na kewaya da shi. A nan ya gamsu cewar zan iya aikin don haka babu wani bata lokaci ya ba ni takardar rajista na cika tare da sa hannun maigidana.

Daga nan na fara hawa titi sosai ina gudanar da sana’ar kamar sauran direbobi.

Da wane abu salon tukinki ya bambanta da na mazan?

Eh, to ni zan iya cewa ba kamar sauran direbobin ba da ke daukar kowane jinsi, ni mata kawai nake dauka. Duk inda mace ke so nakan dauke ta na kai ta, amma ban da maza.

Idan kika ga namiji a babur dina dan uwan ne ko kuma irin wadanda ke son kai labarin sun shiga babur din mace. To wadannan da sun shiga mun yi hoto sai su sauka.

Haka kuma za ki ga tukina a natse nake yi duk da cewa shi tukin wanann babur din dole sai mutum ya koyi sauri idan ba haka ba kuwa akwai ’yan ruftawa wadanda idan ba ka yi da gaske ba to kullum sai sun lalata maka babur.

A yanzu haka na fara koyar ruftawa, haka kuma nakan iya dage kafa daya kamar yadda mazan ke yi.

Haka kuma ni na fi yin tuki da yamma bayan da maigidana ya dawo gida misalin karfe uku sai a bar babur din ya hurta zuwa karfe hudu ni kuma sai na dauka na je na yi zuwa karfe takwas sai na tashi na biya na dauki yarana bayan sun tashi daga Islamiyya sai mu tafi gida gaba daya.

Wadanne nasarori da kalubale kika samu a sana’ar?

Zan iya cewa daga lokacin da na fara zuwa yau ina jin dadin sana’ar, kasancewar duk inda zan shiga sai na samu masoya.

Kai wasu ma za su shiga babur din su biya fiye da kudin da ya kamata su biya saboda suna cewa na burge su.

Ta bangaren ’yan KAROTA kuwa sai dai na yi godiya domin gaskiya suna taimaka min, duk da yake cewa ni ba na karya dokokin hanya. Kin san tukin mata ba su fiye ruftawa ba.

Haka kuma a duk lokacin da babur dina ya yi faci ko mai ya kare ko kuma na shiga wani wuri na makale to insha Allah za ki ga matasa sun kawo min dauki.

Ko ranar nan sai da wani ya daura min aron tayarsa lokacin da tawa ta yi faci.

Haka kuma akwai ranar da mai ya kare a babur din, sai wasu matasa suka je suka sayo man da kudin aljihunsu suka zo suka zuba min. Babu abin da zan ce da jama’a sai godiya.

Tunda na fara wanan sana’a babu wani kalubale da na taba fuskanta Alhamdulillah.

Idan ma akwai kalubale sai na rashin babur, domin a yanzu ina mafani da ta maigidana ne. Dole sai na jira shi ya dawo sanann ni kuma na dauka, abin da aka fi sani da sojan haya.

Mene ne burinki a wannan sana’a?

Ina da burin na ga cewa kamar yadda maza suka mamaye sana’ar, mu ma mata mu fito mu yi ta, domin ba sana’a ce ta maza kawai ba.

Mata suna hawa babur din nan, idan ya kasance mata ne ke tuki to matan nan za su fi jin dadi tare da sakewa a ciki.

A yanzu haka na kuduri aniyar koyar da duk matar da take son yin wannan sana’a. Zan koya mata kyauta.

Burina dai kawai na ga yau mu ma mata muna gudanar da sana’ar don tallafa wa kawunanmu da iyalanmu.

Ina so na ga mata sun daina barace-barace da roke-roke. Kuma idan mace na da sana’a za ki ga matsaloli wadanda ke kawo mutuwar aure sun ragu a tsakanin ma’aurata.

Wane kira kike da shi ga ’yan uwanki masu wannan sana’a?

Kirana gare su shi ne da su ji tsoron Allah su kuma tsaya su rike sana’arsu hannu bibbiyu.

Su kuma zama masu bin dokokin hanya domin tsarkake sana’ar a daina yi mata kallon sana’ar marasa aikin yi.

Wane kira kike yi ga gwamnati?

To ina kira ga gwamnati da ta tallafa mana (mata) da wanann babur din da za mu gudanar da hayar.

A yanzu kudin da ’yan kasuwa suke bayar da mashin din ya yi kudi sosai, muna so gwamnati ta ba mu shi a farashi mai rahusa.

Kin san a yanzu ana biyan Naira dubu 20 zuwa 21 a duk mako. Wallahi ya yi mana yawa.

Muna so gwamnati ko kuma wani mai hannu da shunin su kawo mana baburan nan domin tallafa wa rayuwar mata.

A zauna a yi tsari mai kyau game da yadda za mu rika biyan kudin haya.