Daily Trust Aminiya - Matar aure ta caka wa makwabciyarta kwalba
Subscribe

Matar aure ta caka wa makwabciyarta kwalba

Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa zargin ta da daba wa makwabciyarta fasasshen kwalba.

Matar mai shekara 20 ta caka wa makwabciyar tata kwalba ne a lokacin da wata takaddama ta kaure a tsakaninsu.

’Yan sanda sun gurfanar da ita ne bisa zargin kai farmaki a gaban Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Clement Okuomose ya shaida wa kotun cewa a ranar 10 ga watan Disamban 2020 da misalin karfe 7.30 na dare ne matar ta yi wa makwabciyar tata danyen aikin a yayin sa-in-san.

Sai dai wadda ake tuhumar ta musanta zargin da ASP Clement ya gabatar wa kotun, wanda ya ce laifi ne karkasin sashe na 172 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas, 2015.

Bayan sauraron bayanan bangarorin, Shugaban Kotun, Mai Shari’a Fadahunsi Adefisoye ya ba da belin matar da ake zargin a kan N50,000 kuma za ta kawo mutum daya da zai tsaya mata.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Janairu, 2021.

More Stories