Matar aure ta kashe mijinta kan karin aure | Aminiya

Matar aure ta kashe mijinta kan karin aure

Jami’in dan sanda
Jami’in dan sanda
    Seun Adeuyi da Sagir Kano Saleh 

Wata matar aure ta hallaka mijinta ta hanyar zuba mishi gubar asid saboda zai yi mata kishiya.

Matar ta yi wa mijin nata wanda suka shekara 12 tare wannan danyen aiki ne ranar Lahadi a unguwar Apo da ke Masaka a Jihar Nasarawa.

Majiyarmu a yankin ta ce a baya-bayan nan mamacin mai shekara 42, na yawan samun sabani da matar tasa kan shirinsa na kara aure.

Majiyar ta ce a baya matar ta taba kwashe kayanta daga gidan mijin na tsawon shekara biyar, daga baya shi kuma ya auri wata mata.

Wani kanin marigayin ya ce, “Dan uwana na yawan yin korafi kan matar tasa; wani lokaci ko abinci ba ta ba shi.

“Domin a samu zaman lafiya, sai ya nemi mu yi mata magana, mutane suka zo aka yi mata magana, amma ba ta ce komai ba.

“Ranar Lahadi sai muka ji hayaniya a gidan, sai muka garzaya muka shiga, ko da muka je sai muka samu ta riga ta yi mishi wanka da gubar asid, har jikinsa na zagwanyewa.

“Mun kai shi asibiti amma suka ki karbar shi, shi ne muka kai shi wani wurin, daga baya ya rasu ranar Litinin da safe.”

Wani dan uwan mamacin ya ce sun riga an yi mishi sutura bisa tsarin addinin Musulunci kuma sun shiga neman matar.

Har aka kammala hada wannan rahoto ba a samu jin ta bakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ba.