✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da dan uwanta ya mika ta ga masu garkuwa ta ba da shaida a Kotu

Muna cikin tafiya sai ya saki babbar hanyar ya kama wata karamar hanyar.

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zama a unguwar Dogarawa ta garin Zariya, ta dage ci gaba da sauraron karar da ake yi wa Abubakar Halliru bisa zargin hannunsa a garkuwa da wata ’yar uwarsa zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu 2022.

Aminiya ta ruwaito cewa, ana dai tuhumar Abubakar Halliru kan zargin kai wata ’yar uwarsa wajen masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

A yayin da take bayar da shaidar abin da ya faru a tsakaninta da Abubakar Halliru, Hajiya Binta Muhammad ta yi wa kotu bayanin cewa, shi wanda ake tuhumar dan uwanta ne kuma ta amince da shi matuka don haka a ko yaushe take kyautata masa zato.

A cewarta, la’akari da yadda ta amince da shi shi ya sanya suke harkar kasuwanci inda har ta danka masa kudinta naira miliyan 3 da dubu 98 a hannunsa domin a juya mata.

Sai dai ta ce duk tsawon lokacin da suka shafe suna harkar kasuwancin, ba ta taba neman ya bata wani abu ba sai a ranar 8 ga watan Agusta 2021  data bukaci da ya bata wani kaso daga cikin kudin amma ya yi burus da ita

Ta ce, ya daina daukar wayarta idan ta kira shi, sai a ranar 10 ga watan Agustan bara ne ya kirata yana tambayar inda zai same ta.

“Sai na sanar da shi cewa ina kasuwar Sabon Gari, amma sai ya bukaci da same shi da zummar cewa za mu hadu da wani Alhaji Salisu  unguwar Dan Magaji wanda a wurinsa zai karbi kudina ya ba ni.

“Sai na turje da cewa harka ce tsakaninmu ba sai wani ya shiga ciki ba, don haka na ce ba wurin wanda za ni.

“Amma sai ya kafe a kan lallai sai mun je wurin Alhaji Salisu da ya ce sai in ya ganta ne sannan zai bayar da kudin, wanda daga haka ne sai na yarda na bi shi muka tafi.

“Bayan na kira shi don na tuntubi wurin da za mu hadu, sai ya ce na same shi a shataletalen Kano yana jirana a nan.

“Sai na dauki mota ta na je har wurin na same shi, na kuma mika masa mukullin motar don ya tuka, kuma daga nan muka kama hanya.

“Ko da na ga mun kai Danmagaji bai tsaya ba zai wuce, sai na tambayeshi ya za ka wuce sai ya ce ai Alhaji Salisun ya turo masa da sakon tes cewar ya tafi gida sai dai mu same shi a can.

“Mun kai hanyar da ta nufi Galadimawa sai ya kira waya na ji yana cewa gamu nan zuwa nan da minti 20 za mu iso.

“Sai na ce da shi ai tafiyar minti 20 akwai nisa kuma ga shi an ce hanyar ba ta da kyau, amma ya yi shiru bai ce min uffan ba.

“Muna cikin tafiya sai ya saki babbar hanyar ya bi wata karamar hanyar inda muka hadu da wasu mutane biyu suna tsaye a gefe da gefen hanya rataye da bindiga kirar Ak47 a kafadunsu.

“Sai na razana na nemi ya koma da baya ina ta addu’a, amma ya ki sai da ya kai inda suke ya tsaya kuma suka umurcemu da mu fito.

“Da muka fito daga motar sai suka ce mu zauna daga nan sai wani daga cikinsu ya mare ni suka tisa mu zuwa wajen sauran abokansu da ke gaba inda wani ya karyo itace ya rika dukana.

“Daga nan sai jagoransu ya umurci daya cikinsu da ya daukeni a kan babur ya tafi da ni tsauni, na rika rokon da su hada ni da dan uwana a wuri daya, kuma don Allah kar su yi masa komai nan ma suka ci gaba da dukana sai na hau aka tafi da ni.

“Bayan wani dan lokaci sai ga sauran har da shi dan uwan nawa suka same mu a tsaunin inda suka ce naira miliyan 100 suke so a hannuna, sai na ce musu ba ni da wannan kudin amma su kyale ni kar su taba lafiya ta zan ba su iya abinda nake da shi.

Hajiya Binta ta ci gaba da bayyana wa kotun cewa bayan dare ya soma yi ne sai suka tafi suka bar mutum daya don ya yi gadinta har zuwa safe tare da sanar da ita cewa ta yi tunani kan kudin don idan babu za su kasheta.

Ta ce, Allah cikin ikonsa, sai barci ya fara kama wanda ke tsare da ita sai ta dauki dutse ta yi jifa sai ya tashi firgi-git ya kewaya don ganin ko mene ne, bayan da ya dawo sai ya ce mani da akwai alamun hadari za a yi ruwan sama daga nan sai ya shiga cikin bukkar da tabarmarsa ya kwanta kusa da ni a nan kuma sai barci ya dauke shi.

“Ni kuma da naga haka, sai na lallaba na tsere duk da ana ruwa, amma saboda rashin sanin inda zan nufa sai na fada hannun wasu masu garkuwa da mutane inda suka ce za su taimakeni, koda yake an basu cigiyar wata wadda ta tsere, sai na ce bani ba ce sai suka tafi da ni sansaninsu, a can ne suka ce su na bukatar naira miliyan 30.

“Bayan na kwashe mako takwas a hannunsu, daga nan sai suka ce in ba su lambar da za su yi magana don a kawo musu kudin sai na ba su lambar kuma aka daidaita da su a kan naira Miliyan 5 da dubu 500 da wayar hannu guda 2 da katin waya na naira dubu 70.

“Da aka cika musu bukatunsu ne suka sakoni inda da na ya dauko ni ya wuce da ni asibiti Salama da ke Kwangila inda na kwana hudu ana duba lafiyata saboda sun ce akwai zazzabi mai karfi tare da ni kuma jinina ya yi kasa.

“Bayan an sallame ni daga asibiti sai muka tafi ofishin ’yan sanda da ke Danmagaji inda na shigar da koken abinda ya faru da ni, a cewar