✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar da ke kai wa ’yan bindiga abinci ta shiga hannu a Kwara

An cafke matar tare da masu garkuwa da matar tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Bauchi da Osun, Misis Oladapo Jumoke Bamigboye.

Dubun wata mata da ke yi wa ’yan bindiga safarar garin rogo da sauran kayan masarufi a Jihar Kwara ta cika.

’Yan sanda sun cafke matar ce tare da wasu maza uku da ake zargi da yin garkuwa da matar tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Bauchi da Osun, Misis Oladapo Jumoke Bamigboye.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce, “An gano  matar ce ke kai wa ’yan bindiga garin rogo da sauran kayan abinci da suke amfani da su wajen ciyar da mutanen da suka ka yi garkuwa da su.”

Tuni dai aka kubutar da Misis Bamigboye bayan an biya kundin fansa, kamar yadda mijinta, Kanar Theophilus Bamigoye (murabus) ya tabbatar.