✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar DCP Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a kotu

Ta ya ke jikin ta fadi ne lokacin da kotun ta dage sauraron bukatar bayar da belin mijinta

Matar dakataccen dan sandan nan da aka gurfanar a gaban kotu kan zargin hada-hadar miyagun kwayoyi, DCP Abba Kyari, wato Ramatu Kyari, ta yanke jiki ta fadi a ana tsaka da zaman kotun ranar Litinin.

Rahotanni sun ce Ramatun ta fadi ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da aka dawo ci gaba da sauraron karar da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shigar da mijinta.

Ta fadi ne a kasa jim kadan bayan alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya jinkirta yanke hukunci kan bukatar bayar da belin Abban da wasu mutum shidan da ake tuhumarsu tare.

Matar, wacce ke sanye da bakin Hijabi ta fadi ne lokacin da jami’an NDLEA ke kokarin ficewa da mijinta daga harabar kotun.

Kodayake an kwashe ta ranga-ranga, wasu jami’an NDLEA da wasu lauyoyi sun garzaya da ita zuwa daya daga cikin ofisoshin kotun.

Wasu makusantanta sun ce dama tana fama da ciwon Asma, kuma shi suke zaton ya tashi lokacin da ta fadin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, ana ta kokarin samo mata na’urar shakawa (inhaler), don a samu ta farfado.

A ranar Litinin ne dai NDLEA ta roki kotun da kada ta amince da bukatar lauyoyin Abba Kyari ta ba da belinsa.

NDLEA dai ta ce in aka ba da belin nasa zai cika wandonsa da iska zuwa kasashen waje.