✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Sarkin Benin ta haifi ’yan hudu

Oba Ewuare II ya yi maraba da zuwa ’yan hudu da matarsa ta biyar ta yi.

Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya yi maraba da haihuwar ’yan hudu da amaryarsa, Sarauniya (Oloi) Aisosa Ewuare II, ta yi.

Oba Ewuare II ya sanar da hakan ne a fadarsa da ke Benin a ranar Juma’a, yana mai godiya ga Allah Madaukakin Sarki kan baiwar da Ya yi masa.

’Yan hudun da har yanzu ba a ambaci sunayensu ba sun hada namiji daya da mata uku da namiji daya.

Tuni sarkin ya kuma bayyana cewa fadarsa za ta gudanar da biki na musamman don murnar samun haihuwar ’yan hudu da matar tasa ta yi.

Mai jego Oloi Aisosa Ewuare II ita ce karama daga cikin jerin matan sarkin na Benin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa a watan Mayu, 2020, ne Sarauniya (Oloi) Iyayota Ewuare II ta haifa wa Oba Ewuare dansa na farko bayan ya gaji sarautar kakanninsa a matsayin Sarki na 40 a Masarautar Benin.