✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar tsohon Shugaban Kasa Shagari, Hadiza ta rasu

Hajiya Hadiza Aliyu Shagari ta rasu baya fama da rashin lafiya.

Hajiya Hadiza, matar tsohon Shugaban Kasa Shehu Usman Aliyu Shagari ta rasu bayan fama da rashin lafiya.

Sanarwar da iyalan suka fitar ta ce Hajiya Hadiza Shehu Shagari ta rasu ranar Alhamis tana da shekara 80, bayan fama da cutar COVID-19.

Sanarwar na fatan za yi jana’izarta da yammacin ranar Alhamis.