✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa 172 sun haukace saboda shan kwaya a Zamfara

Shan miyagun kwayoyi ya haukata matasa 172 a Jihar Zamfara cikin shekara shida da suka gabata. Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa…

Shan miyagun kwayoyi ya haukata matasa 172 a Jihar Zamfara cikin shekara shida da suka gabata.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta sanar da haka a jihar ta bakin mataimakin kwamandanta na sashen yaki da miyagun kwayoyi na jihar, Ladan Hashim.

Ladan ya ce, “Matasa da dama na tsare a gidajen yari, wasu a gidajen kula da lafiya, yawancinsu kuma na fama da cututtukan kansar makogwaro, cutar hanta da cutar koda da sauransu.

“Mafita ita ce a tabbatar da cewa kowa yana amfani da magunguna yadda ya dace kamar yadda kwararrun likitoci suka tsara mana,” inji shi.

Ya ce a cikin wata taran da suka gabata hukumar ta tsare mutum 221 kan shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar, ta kuma yi wa wasu 152 jan kunne.

“Saboda haka akwai bukatar hadin kai, fahimta da taimako domin bayar da dauki a kan kari da yi msusu magani da kuma dawo da su cikin al’umma.

“Dukkansu suna bukatar samun daukin da ya dace a wurin da ya dace kuma a kan lokaci.”