✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Matasa ku daina raina sana’a’

Abubuwan da za ku yi domin samun nasara a sana'o'inku.

Mai yi wa masu karatu za su iya tunawa da wani matashin dan jarida mai digri da ke tuyar kosai a Maiduguri babban birrin Jihar Borno.

Daya daga cikin dalilan da Sunday Williams Omega ya bayar na yin wannan sana’a shi ne: nuna wa matasa cewa kar su raina sana’a komai kankantar ta.

Akwai dalilai da dama da kan sa matasa raina sana’a, kama daga rashin hukuri da juriya zuwa mutuwar zuciya , da raina riba da sauran su.

Amina Muhammad ’yar kasuwa ce da ke harka a kafofin sadarwa na zamani take kuma koya wa matasa sana’a.

Sai an yi hakuri

A ganinta sai da hakuri da juriya za a samu abin da ake nema.

“Na farko dai sana’a tana bukatar hakuri da juriya saboda sana’a a rayuwa ba abu ne mai sauki ba.

“In za ka yi sana’a ya zama kana da hakurin hakuri da hakuri”, inji ta.

Hajiya Amina, wacce aka fi sani da amwa_collections a Instagram, ta kuma bayyana abu na gaba da ya sa matasa ke raina sana’a.

“Na biyu kuma mutuwar zuciya: zuciyarsu ta mutu sai ku ga mutane ba su da kishin zuci da za su tashi su nemi na kansu;  sun gwammace su yi ta rage murya suna roko a ba su”.

Ta kara da cewa, “sai ku ga yanzu mutum ya zo yana so ya yi sana’a amma kuma ba ya so ya motsa jiki, baya son ya kuma kashe kudi, amma yana so ya samu riba.

“To kun ga ita sana’a ba za ta yiwu a haka ba; idan kana so ka ci riba a rayuwa dole kai ma sai an taba ta ta wani gefen”, inji Hajiya Amina.

Cigaban zamani

Ta kuma ce yanzu zamani ya zo da wasu sauye-sauye da za su taimaka wa matasa wajen san’a ba sai sun sha wahala ba.

“Misali yanzu kuna sana’a, a ce mutane da yawa ba su san kuna yi ba, watakila bai fi ’yan uwanku ko abokan arziki ba ne kawai suka san kuna yi; dole sai kun yi talla kuma shi tallan ai ba kyauta ba ne dole sai an cire kudi.

“Kamar yanzu ma yawancin sana’a ta koma kafofin sadarwa na zamani kamar su Instagram, Facebook, Twitter, Whatsapp da dai sauran su – yanzu haka a Instagram akwai abin da ake kira sponsored advert dole sai ka biya su kudi a yi maka talla har mutane su gani su san kana sayar da kaya har su zo su saya”.

“To duk wadannan su ne abubuwan da suka sa mutane ke raina sana’a, ba su kuma dauke ta da mahimmanci ba”.

Daga nan sai Hajiya Amina, wacce ta yi shekara shida tana saye da sayarwa ta intanet, ta shawarci matasa da cewa zaman jiran aiki ba nasu ba ne.

“Shawarar da zan ba matasa a nan ita ce su daina raina sana’a ko yaya take; ba ku sani ba ko hanyar arzikinku a ciki take in Allah Ya albarkace ta.

“Sana’a tana da matukar amfani a rayuwa kuma tana taimako ta hanyoyi da dama. Ga sana’o’i nan da dama sai wanda kuka zaba; matasa ku tashi ku nemi na kanku”, inji ta.