✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa masu fashi da bindigar roba sun shiga hannu a Ogun

Lamarin ya faru ne a Abeokuta babban birnin jihar

Wasu matasa biyu da ke kokarin yin fashi da bindigar roba sun shiga hannuun ‘yan sanda a jihar Ogun

Lamarin ya faru ne a unguwar Adesan da ke yankin Mowe a Abeokuta babban birnin jihar, ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Abimbola Oyeyemi a hirar sa da ’yan jarida, ya ce, Chioma Okafor mai shekara 29 da Nweke Joshua sun tsare wani mai suna Johnson Nwokoro da kananan bindigogi a inda suka yi masa fashi.

Matasan sun shiga hannu ne bayan da ‘yan sandan suka samu rahoton cewa, wasu ‘yan fashi sun kai hari kantin, titin Adesan, inda ‘yan sandan cikin gaggawa suka tura jami’ansu, a inda suka kama matasan biyu.

“A bincikenmu, sai muka fahimci cewa sun zo kantin ne yin fashi da makami dauke kananan bindigogi na bogi, masu kama da na gaske” inji Kakakin rundunar.

Nweke Joshua mai shekara 19 ya ce, Chioma ce ta ba su shawarar yin haka, ta kuma sayo musu bindigogin robar don yin fashi a kantin mutumin.

Matashin ya ci gaba da cewa, sun shiga kantin ne kamar masu sayen wani abu, sai kawai suka fito da bindigogin, suka kuma tsare mai kantin, tare da neman ya ba su kudin da ke wurinsa, ana haka kuma ‘yan sanda suka zo.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Lanre Bankole, ya umarci a mika matsan zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar don ci gaba da bincike.