✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun banka wa ’yan fashi wuta a Ibadan

’Yan sanda na binkicen gano dalilin matasan na yin danyen hukuncin.

Wasu fusatattun matasa sun banka wa wasu mutum biyu wuta kan zargin su da fashi da makami a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Mutanen da ake zargin ’yan fashi ne, an kone dayansu ne a madakatar mota ta ASAS, dayan kuma an kone shi a yankin Oke Addo.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbemiga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce jami’an Amotekun sun ceto daya daga mutanen a hannun matasan.

Fadeyi, ya kara da cewa rundunar tasu ta fara bincike don gano dalilin da ya fusata matasan har suka dauki hukunci a hannunsu.

Sai dai ya ce Rundunar ba za ta lamunci daukar doka a hannu ba, domin a cewarsa kotu ce kadai ke da hurumin tabbatar da laifin mutum.