✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun tare gwamna kan kisan mutum 88 a Kebbi

Masu zanga-zangar sun tare gwamnan jihar a kan hanyarsa ta zuwa gaisuwar ta’aziyya.

Matasa sun fusata da kisan mutum 88 da ’yan bindiga suka yi a Jihar Kebbi a ranar Alhamis, inda suka yi zanga-zanga.

Fusatattun matasan sun tare wa gwamnan jihar, Atiku Bagudu hanya, a yayin da ya je yin ta’aziyyar kisan mutanen da ’yan bindiga suka yi a garin Riba.

  1. Ana kashe N211m wajen kwashe shara duk wata a Kaduna —Kwamishina
  2. Soja ya kashe jami’in DSS saboda dan damfara
  3. Ana kashe N211m wajen kwashe shara duk wata a Kaduna —Kwamishina

Sun kuma cinna wa wata mota wuta, sai dai ba a samu cikakken rahoto kan motar da suka kona ba.

Matasan sun fito kan titi suna kona tayoyi ne a ranar Asabar domin nuna bacin ransu kan kisan kiyashin da suka ce ’yan bindiga ke wa mutane a Jihar.

A ranar Alhamis ne ’yan bindiga suka kai hare-hare a wasu kauyuka takwas na Karamar Hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, suka kashe mutum 88.

Mai magana da yawun Gwamna Bagudu, Yahaya Sarki, bai daga waya ko amsa rubutaccen sakon da aka aike masa ba game da kisan mutanen da ’yan bindigar suka yi.

Shi kuma kakakin ’yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya ce zai nemi wakilinmu da zarar ya kammala hada rahoton da yake hadawa a kan zanga-zangar.