✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun yi wa gwamnanti rubdugu kan shigo da masara

Kudin da za a kashe wurin shigo da masara daga waje ya isa a farfado da nomanta a Najeriya, inji NYFN

Matasan Najeriya sun caccaki Gwamantin Tarayya kan bayar da izinin shigo da masara kasar daga kasashen ketare.

Kungiyar Matasan Manoma (NYFN) ta ce matakin zai gurgunta jarin miliyoyin ’ya’yanta wadanda idan suka samu tallafi za su samar da wadatacciyar masar a kasar.

“Muna bayyanawa karara cewa Kungiyar Manoma Matasa ta Najeriya na adawa da shigo da hatsin cikin kasar ba”, inji Darakta Janar na NYFN, Promise Amahah.

In za a iya tunawa Babban Bankin Najeirya (CBN) ya umarci manyan ’yan canji su daina bayar da takardun karbar canji ga masu shigowa da masara daga kasashen waje.

Daga baya CBN ya janye umarnin sakamakon karancin masara a Najeriya.

– Illar shigo da masara da waje –

Hukumar kwastam ta Najeriya a cikin wata sanarwa ta tabbatar da cewa an yi wa wasu kamfanoni hudu sassaucin shigo da ton 262,000 na masara.

Kamfanonin sun ne Wacot Limited, Chi Farms Limited, Crown Flour Mills da kuma Premier Feeds Company Limited.

Sai dai a martaninsu NYFN ta ce damar da aka ba wa kamfanonin za ta karya manoman Najeriya.

Maimakon haka a cewarta, kamata ya yi kamfanonin sun tallafa wa matasan manoma su noma karin hatsin a kasar.

“Kudin da za a kashe wurin ba wa kamfanonin canjin kudaden kasashen waje ya isa a ba wa matasan manoma su noma masara a fadin Najeriya”, inji shi.

Sanarwar ta ce tallafa wa matasan manoma zai bunkasa asusun ajiyar Najeriya a kasashen waje da ke cikin matsi sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.