✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Arewa 500 na kasuwancin rake a Ibadan

Daruruwan matasan Arewa masu ci-rani ne suka amfana da wata karamar kasuwar rake a birnin Ibadan, Jihar Oyo. Aminiya ta ziyarci kasuwar da ke wani…

Daruruwan matasan Arewa masu ci-rani ne suka amfana da wata karamar kasuwar rake a birnin Ibadan, Jihar Oyo.

Aminiya ta ziyarci kasuwar da ke wani bangare na babbar kasuwar Dugbe a domin ganin yadda harkoki ke gudana.

Wakilinmu ya iske matasan sun dukufa wajen kankare dami-damin rake suna ferewa suna yankawa kafin su sayar domin dogaro da kai.

“Shekara bakwai ke nan da muka bude wannan kasuwa da ta samar da guraben ayyuka da sana’o’i ga matasanmu daga Arewacin kasar nan.

“A kowane garin Allah Ya waye za ka taras da matasa fiye da 500 suna hada-hadar rake cikin wannan kasuwa.

Wani sashen na masu sayar da rake a Kasuwar Dugbe da ke birnin Ibadan
Wani sashen na masu sayar da rake a Kasuwar Dugbe da ke birnin Ibadan

“Cikinsu akwai manoman rake a kauyukan Apata, Alomaja da Alakiya da ke kusa da Ibadan da dillalai masu sayowa suna sayarwa ga masu yawo a kan hanya.

“Yanzu haka muna kokarin gano hanyar da za mu kusanci gwamnati ta taimaka mana kamar yadda ta saba yi wa kananan ’yan kasuwa domin bunkasa wannan harka”, inji Shugaban kasuwar, Alhaji Muhammadu Maiwake.

Daya daga cikin dillalan raken cewa ya yi, “Idan muka sayo daga manoma muna sayarwa ne ga ’yan uwanmu da suke gyarawa domin shiga cikin gari da kasuwanni da suke sayarwa ga jama’a.

“Idan sun dawo su biya mu ba tare da matsala ba kuma haka muke tafiyar da kasuwar cikin adalci”.

Aminiya ta zanta da wasu masu yawon sayar da rake a cikin gari inda suka ce, “Muna yin hayar baro ne da muke daukar raken da muka gyara domin shiga cikin kasuwanni —muna biyan Naira 500 kudin hayar baro daya a kowane mako.

“Kasuwa tana tafiya daidai gwargwado sai godiya ga Allah domin dukkanmu mun dogara da wannan sana’a ne wajen samun abin da za mu ci da iyalinmu”.