✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Arewa na goyon bayan mulki ya koma yankin Yarabawa a 2023

Sun ce za su juya wa duk jam'iyyar da ta fitar da dan takara daga Arewa maso Yamma baya

Matasa daga yankin Arewacin Najeriya sun shawarci jam’iyyar APC mai mulki da ta ba wa yankin Kudu maso Yamma takarar Shugaban kasarta a babban zaben 2023.

Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYFL) ce ta yi kiran tare da rokon ’yan yankin masu son yin takarar Shugaba Kasa a 2023 da su janye.

“Muna rokon shugabannin yankin Arewa maso Yamma da su jingine duk wata aniyar tsayawa takarar Shugaban Kasa ko Mataimakin Shugaban Kasa a 2023 domin a samu hadin kan Arewa.

“NYLF mai tarin mambabo da magoya baya a Arewa maso Yamma ta yanke shawarar kin zaben duk jam’iyyar da ta tsayar da dan takarar Shugaban Kasa ko mataimakinsa daga Arewa maso Yamma”, inji ta.

NYFL da aka kafa tun 1992 tare da wasu kungiyoyin matasan Arewa 42 na daga cikin wadanda ke kan gaba wajen goyon bayan ’yan takarar da suka fito daga Arewa.

Da yake jawabi, Shugaban gamayyar kungiyoyin, Kwamaret Eliot Afiyo ya bukaci APC da ta mutunta yarjejeniyar mulkin karba-karba da ta kulla na cewa mulki zai koma Kudu maso Yamma a 2023.

“Saboda yaka muke shawartar APC da ta fito da dan takararta daga Kudu maso Yamma”, inji jawabin da da ya yi a Yola, Jihar Adamawa.

Kungiyar ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan zai fito takara a 2023, tana mai cewa Arewa ba za ta goya masa baya ba.