✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Arewa sun yaba wa Buhari kan dakatar da Twitter

Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas, MNYOF, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakin dakatar da kafar sadarwa ta Twitter a kasar nan bisa zargin shafin…

Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas, MNYOF, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakin dakatar da kafar sadarwa ta Twitter a kasar nan bisa zargin shafin da rura wutar tashin hankali.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham, wanda ya bayyana hakan a yayin zantawa da ’yan jarida a ranar Alhamis a Abuja, ya bukaci gwamnatin da ta jajirce a kan matakin, har sai kamfanin ya cika sharuddan kasar nan kan al’amuranta na tsaro.

Kungiyar ta nuna kaduwarta kan matakin share wani sashi na bayanin tsawatarwa da Twitter ya yi na sakon da Shugaban Buhari ya wallafa a shafin, yayin da a gefe guda Twitter ke barin wadanda ake zargi da kai hare-hare kan kafofin gwamnati na cin karensu babu babbaka.

Shugaban kungiyar ya yi maraba da sanarwar da Ministan Yada Labarai Alhaji Lai Muhammad ya yi a ranar Laraba na cewa gwamnati za ta fara yi wa kafofin sada zumuntan irin su Facebook da Twitter da Instagram rajista kafin su ci gaba da gudanar da ayyukansu Najeriya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham

Ya yi misali da tarar Dala miliyan 267 da kasar Faransa ta yi wa kamfanin matambayi baya bata na Google a kasar.

“Barin abubuwa kara zube shi ne yake ba su damar cin karensu babu babbaka a kasashen Afrika da a wani zubin ke jawo tashin hankali.

“Akwai lokacin da aka rufe daukacin kamfanonin sadarwa a jihohi uku na yankin Arewa maso Gabas da ke karkashin dokar ta baci da gwamnatin baya ta yi domin samar da tsaro, wanda kuma hakan ya yi tasiri.

“Ina mamakin yadda wadansu a yanzu ke korafin cewa dakatar da kamfanin Twitter take ’yancin fadar albarkacin baki ne, duk da barazanar da hakan ke iya yi ga bangaren tsaro.’’

Shugaban matasan ya ce akwai kasashe kimanin bakwai da suka rufe kafar Twitter dungurugum a kasashensu, alhali matakin da Najeriya ta dauka na wucin gadi ne.