✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasan da suka karkatar da kayan N25m sun shiga hannu

An gurfanar da wasu mutane 23 da ake zargi da satar mutane da fyade da fashi da makami.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta ce ta kamo wasu matasa bakwai da take zargi da karkatar da kayan sakawa na siyarwa da suka kai N25m.

Kakakin rundunar, SP Adewale Osifeso ne ya bayyana hakan a ganawarsu da manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa baya ga matasan an gurfanar da wasu mutane 23 da ake zargi da satar mutane, da fyade, da fashi da makami.

Sauran wadanda aka kamo sun hada da masu shirya takardun aiki na jabu, da sauran manyan laifuka a jihar.

Osifeso ya kuma ce wadanda ake zargi da karkatar da kayayyakin an kamo su ne a ranar 16 ga watan Oktoba da misalin karfe 3:00 na rana, yayin da rundunar ke gudanar da sintiri a garin Ogbomoso.

Ya ce rahotannin sirri da suka samu ne ya kai su ga gano mutanen, bayan gano su a Ogbomoson cikin wasu motoci biyu makare da kayan da suka karkatar.

“Daga nan ne ’yan sandan suka kamo mutane biyar daga cikinsu, da daurin kaya 100 na kayan sakawa daban-daban.

“Wadanda a ke zargin sun amsa laifinsu, kuma sun ba mu bayanan inda sauran biyun suke suma mun kamo su,” in ji shi.