✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Najeriya sun gabatar da kansu domin taya Ukraine ta yaki Rasha

Matan Najeriya sun mika gwamnatin Ukraine sunayensu domin zama mayakan sa-kai a yakinta da Rasha

Wasu matasan Najeriya sun gabatar da kansu domin zama mayakan sa-kai da za su taimaka wa kasar Ukraine yakar Rasha da ta far mata da yaki.

Matasan sun yi dafifi ne a Ofishin Jakandancin Ukraine da ke Abuja, inda suka rika sanya sunayensu a takardar rajistar da ofishin ya tanada.

Ana ganin mika wuyan da matasan suka yi amsa kira ne ga Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, wanda ya bukaci al’ummar duniya da su taimaka wa kasarsa wajen yakar Rasha wadda ta kaddamar da yaki a cikin kasarsa.

A sanarwa da Mista Zelenskyy ya fitar a ranar Lahadi, ya jijina wa al’ummar Ukraine nisa irin jarumtar da suka nuna wajen tsayuwa kai da fata su kare kasarsu.

Sanarwa da Mista Zelenskyy ya fitar kwana uku bayan mamayar ta Rasha a kasarsa, ta zargi sojojin Rasha da kashe fararen hula a Ukraine.

Daga nan sai ya kirayi duk mai son bayar da gudunmuwa wajen kare Ukraine daga ko’ina a fadin duniya, ya zo su yi taron dangi tare da mutanen Ukraine wajen yakar Rasha.

Ba yanzu ba

Sakatare na Biyu a Ofishin Jakadancin Ukraine a Neriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da zuwan matasan ofisin domin a dauki sunayensu a matsayin mayakan sa-kai zuwa Ukraine.

Sai dai kuma Mista Bohdan Soltys ya shaida wa kafar yada labari ta The Guardian cewa kawo yanzu kasarsa ba ta yanke shawara game da daukar mayakan sa-kai ba tukuna.

Amsa kiran Ukraine

Idan za a iya tunawa, a sanarwa da Mista Zelenskyy ya fitar kwana uku bayan mamayar da Rasha ta kaddamar a kasarsa ranar Alhamis, ya zargi sojojin Rasha da kashe fararen hula.

Daga nan sai ya kirayi duk mai son bayar da gudunmuwa wajen kare Ukraine a ko’ina yake a fadin duniya, ya zo su yi wa Rasha taron dangi.

A cewarsa, yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine ba mamaya ba ce kadai, yaki ne da tsarin dimokuradiyya da kuma ’yancin dan Adam.

Fakewa da guzuma

A kan haka ne wasu ke ganin cewa matasan da ke mika sunayen nasu suna ganin yakin da Rasha ke yi a Ukraine zalunci ne, shi ya suke neman zuwa su sayar da ransu domin yakar cin zali.

Sai dai kuma wasu na ganin ba da zuciya daya matasan Najeriyan ke neman tarar aradu da ka domin zuwa kasar Ukraine da ke fama da yaki a halin yanzu ba.

A cewarsu, hankali ba zai dauka ba a ce dan wata kasa na kokarin zuwa wata kasa da ’yan asalin kasar da kuma ’yan Najeriya mazauna can da suka makale suke neman a dawo da su gida cikin gaggawa saboda barkewar yakin.

Wani matashi da ke zargin matasan da neman cin bulsu ya ce, “Wannan ba komai ba ne face wata dabara da matasan ke son amfani da ita su tsallaka zuwa kasashen Turai a bagas, sannan su yi layar zana.”

Wani matashi mazaunin Abuja da Aminiya ta zanta da shi ya ce, “Duk da cewa ba lallai ba ne idan ka kwashe su aka kai Ukraine din su tsira da ransu, amma na tabbata suna zuwa kasar za su fara naman yadda za su kara gaba.”

“Ba yaki za su je yi ba, kawai so suke su yi amfani da damar a kai su Turai, daga nan kuma sai a neme su a rasa.” inji shi ma wani matashin.

Ci-rani a Turai

Wannan zargin ba zai rasa nasaba ba da yadda matasa daga kasashe masu tasowa — irin Najeriya da  sauran kasashen Afirka da Asiya — suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai domin samun sauyin rayuwa.

Yawancin matasan da ke zuwa Turai ci-rani daga kasashe masu tasowa suna bi ne ta barauniyar hanya ta  hannun masu fasakwaurin mutane da rubabbun jiragen ruwa.

Wasu daga cikinsu kan kamu da cututtuka — ko su mutu a kan teku — ko su kare a sansanonin bakin haure, bayan wasan bera da mage tsakaninsu da jami’an tsaro a kan iyakokin kasashen da suke shiga ba bisa ka’ida ba.

A wasu lokutan kuma, wasu kan fada a hannun masu safarar bil Adama, inda suke karewa ana sayar da su a matsayin bayi, ana cire sassan jikinsu, kamar koda da sauransu, ana sayarwa masu nema da dan karen tsada.

A wasu lokuta akan tilasta wa mata daga cikinsu yin karuwanci — duk ba tare da su din sun amfana da kudaden da ake samu a kansu ba.

Duk da haka, akwai ’yan Najeriya da sauran kasashe masu tasowa da ke zuwa kasashen Turai ta halastaciyyar hanya domin neman halaliyarsu ta hanyar kasuwanci ko aikin ofis da sauransu.