✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya bar aikin soja saboda wasan barkwanci

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta amince da murabus din da ya yi daga aiki.

Shahararren dan wasan barkwancin nan na Intanet, Abdulgafar Ahmad, wanda aka fi sani da Cute Abiola ya bayyana barin aikinsa da Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya domin ya samu sararin mai da hankali a kan sana’ar da a yanzu ita ya fi so, wato sana’ar wasan barkwanci a kafafan sada zumunta.

Matashin ya rubuta aje aikin soji a shafinsa na Facebook inda ya yaba wa Rundunar Sojin Ruwan tare da Babban Kwamandan Rundunar bisa amincewarsu da aje aikin da ya yi.

A cewarsa, Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta amince da murabus din da ya yi daga aiki, domin ya mai da hankali sosai a kan wasan barkwancinsa da ya sa a gaba a kafafen sadarwar zamani.

Dan wasan barkwancin ya bayyana cewa aikin sojan ruwa ya taimaka masa da horon da ake bukata domin samun nasarar rayuwa.

“Tare da godiya yawa, ina matukar godiya ga Rundunar Sojin Ruwan Najeriya da ta ba ni wannan dama ta aiwatar da horon da ake bukata don ci gaban rayuwa da kyawawan dabi’u, da kuma da’a.

“Samun horarwa a wurin ya nuna min cewa ba shakka ina da hankalin da ake bukata domiin ci gaban dan Adam, da kuma ci gaban rayuwa mai yalwa” inji Cute Abiola.

Matashin ya mika godiyarsa ga Babban Hafsan Sojin Ruwa, Bayis Admiral Awwal Zubairu Gambo, da sauran manyan jami’ansa, inda ya yi kira ga magoya bayansa su hada kai da shi wajen jajircewa domin bayar da gudunmawa wajen bunkasa sana’arsa ta wasan kwaikwayo a Intanet.

Ya ce, “Na yi mamaki game da amincewa da murabus dina daga Rundunar Sojin Ruwa da Babban Hafsan Sojin Ruwan ya yi don in samu isasshen lokacin da zan bi don cika burina.”

Cute Abiola ya bayyana cewa duk da cewa ya yi murabus daga aikin sojan ruwa zai ci gaba da zama jakadansu nagari a gida da kuma kasashen waje.

“Har yanzu ina cikin dangin sojojin ruwa na Najeriya, kuma na yi alkawarin ci gaba da wakilci nagari a Najeriya ko a kasashen ketare.

“Ina alfaharin yin aiki a Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya” inji shi.

Murabus din dan wasan barkwancin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Gwamnan Jihar Kwara Alhaji Abdulrahman Abdulrazak ya nada shi a matsayin mai taimaka masa na musamman kan masana’antu da kere-kere.

A watan Nuwamban bara ne Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta tsare dan wasan barkwancin na wasu kwanaki a matsayin hukuncin da ya saba wa dokar soja ta hanyar sanya wani hoton bidiyo da ya yi sanye da kayan soja a shafukan sada zumunta, lamarin da aka ce ya saba wa manufofin rundunar.