Matashi ya daina cin abinci saboda soyayyar ’yar fim, Hadiza Muhammad | Aminiya

Matashi ya daina cin abinci saboda soyayyar ’yar fim, Hadiza Muhammad

Jarumar Kannywood Hadiza Muhammad
Jarumar Kannywood Hadiza Muhammad
    Abdullahi Abubakar Umar

Wani saurayi ya ce ya gagara ci da sha saboda soyayyar da ya ke yi wa fitacciyar Jarumar Kannywood, Hadiza Muhammad.

Saurayin mai suna Farouq Abdullahi Tukuntawa, ya aike da sakon soyayyarsa zuwa ga jarumar ta shafinsa na Facebook inda ya roke ta da ta taimaka ta ceto rayuwar shi daga kogin soyayyar  da ya dade da fadawa  ciki.

Wata jaridar mai suna Manuniya ta rawaito cewa matashin  ya aika da sakon neman amincewar jarumar a matsayin wadda yake so ya aura  a dandalin sada zumunta na Facebook.

Ya bayyana cewa, ya dade yana so ya bayyana mata irin son da ya ke yi mata, ko da kuwa za ta dauki hakan a matsayin shirme.

A sakon nasa ya ce “Aminci a gareki. Hajiya Hadiza, hakika na dade ina rokon Allah madaukakin sarki ya nuna min kwatankwacin wannan rana kafin na koma gareShi; Ranar da zan furta maki abun da ya dade a raina ko da kuwa za ki dauki hakan a matsayin shirme.

“Zan yi farin ciki da hakan domin na san na yi wa zuciyata babban gata na fitar mata da ciwon da ta dade ta na dawainiya da shi,” inji matasahin.

Daga karshe, ya nemi jarumar da ta ceci rayuwarsa ta  tsamo shi daga kogin soyayyar da ya fada.

“Ba na iya cin abinci, ba na iya barci. Ko da na kwanta, hoton kyakkyawar fuskarki ne kawai ya ke min yawo a ido na.”