✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya fasa fadar basarake ya saci buhuhunan shinkafa a Ekiti 

Kayan da aka sace sun kai N2m a kiyasce

An gurfanar da wani matashi a Kotun Majistare mai zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, bisa zargin fasa fadar Sarki Bobade Adeleke da ke Ire-Ekiti tare da sace buhuhunan shinkafa.

Ana zargin matashin ne da laifuka biyu na sata da kuma barna da gangan.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Sodiq Adeniyi, ya fada wa kotun cewa wanda ake zargin tare da wasu abokan cin mushensa sun aikata laifukan ne ranar 10 ga Agusta, 2022 a yankin Ire-Ekiti.

Adeniyi ya yi zargin mai kare kansa tare da abokan nasa da suka tsere sun saci sarkoki da buhuhunan shinkafa da tukunyar gas mallakar sarkin wanda a kiyasce kudinsu ya kai Naira miliyan biyu.

Ya ce laifukan sun saba wa sassa na 302(1) (a) da 363 na dokokin manyan laifuka na Jihar Ekiti na 2021.

Sai dai matashin ya ki amsa tuhumar da ake yi masa.

Lauyan wanda ake tuhuma, Mista Busuyi Ayorinde, ya bukaci kotun da ta ba da belin wanda yake karewa, tare da alkawarin zai gabatar da shi duk lokacin da aka bukace shi.

Alkalin Kotun, Misi Dolapo Kay-Williams, ta ba da belin matashin kan N500,000 da shaidu guda biyu.

Kana ta dage shari’ar zuwa 6 ga Maris.

(NAN)