✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya jefa tsohuwa mai shekara 80 cikin rijiya a Kano

Ya jefa ta a rijiyar ne bayan ya kada mata suka

’Yan sanda a Jihar Kano sun cafke wani matashi mai shekara 25 da ake zargi da kashe wata tsohuwa mai kimanin shekara 80 a duniya, ta hanyar jefa ta a rijiya bayan ya lakada mata duka.

Ana zargin matashin mai suna Naziru Magaji, mazaunin kauyen Kununu Yalwa Danziyal da ke Karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar ne  Kano da yin aika-aikar ne a kan tshohuwar mai suna Habiba Abubakar, bayan ya yi mankas da kayan maye.

Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama matashin a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

A cewarsa, “Da misalin karfe 1:30 na ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, 2022, mun samu korafi daga wani mazaunin kauyen Wangara da ke Karamar Hukumar Tofa a Jihar Kano cewa da misalin karfe 12:00 na ranar, wani matashi mai kimanin shekara 25 mazaunin kauyen Kununu Yalwan Danziyal a Karamar Hukumar Rimin Gado da ke Kano, ya lakada wa yayarsa, Habiba Abubakar, mai kimanin shekara 80 duka, sannan ya jefa ta a rijiya.

“Da samun labarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shuaibu Dikko, ya umarci jami’ai karkashin jagorancin CSP Isyaku Mustapha da kuma Baturen ’Yan Sanda na Tofa su je wajen.

“Da zuwansu suka ciro tsohuwar daga rijiyar, sannan suka garzaya da ita Babban Asibitin garin Tofa, inda likitoci suka duba ta, sannan suka tabbatar da rasuwarta.

“Binciken farko-farko ya nuna mana wanda ake zargin ya ce yana da tabin hankali, kuma sai da ya yi mankas da kayan maye kafin ya aikata danyen aikin,” inji sanarwar.

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya ba da umarnin mayar da lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar.

Ya ce da zarar sashen ya kammala bincikensa za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu don ya girbi abin da ya shuka.