Matashi ya kashe kansa a Ribas | Aminiya

Matashi ya kashe kansa a Ribas

Gawa
Gawa
    Victor Edozie, Fatakwal da Bashir Isah

Wani matashi mai suna Sunday Orime mai kimanin shekara 21, ya kashe kansa a Jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da daddare a mazauninsa da ke Mile 3 a yankin Diobu na birnin Fatakwal.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa babu wani cikakken bayani kan dalilin da matashin ya dauki wannan mataki a kansa.

Babban jami’in tsaro a kauyen Nkpolu Oroworukwo da ke Fatakwal, Kwamred Godstime Ihunwo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, bayan da labarin aukuwar hakan ya isa gare shi, daga nan ya hanzarta sanar da ‘yan sanda, kuma daga bisani aka dauki gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki.

Ya zuwa hada wannan labarin, kakakin ‘yan sandan jihar da aka nemi jin ta bakinta, DSP Grace Iringe Koko, ba ta ce komai a kan lamarin ba.