✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da kanwarsa a Kano

Matashin ya shiga hannun 'yan sanda yayin da yake kokarin sulalewa daga Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta cafke wani matashi mai shekara 20 bisa zarginsa da kashe kishiyar mahaifiyarsa da kanwarsa ’yar shekara takwas.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.

“A ranar 7 ga Janairu da misalin karfe 11:30 na dare mun samu kiran waya daga wani Sagir Yakubu daga unguwar Rijiyar Zaki.

“Ya bayyana mana cewar ya dawo gida ya tarar da matarsa mai dauke da juna biyu, Rabi’atu Sagir mai shekara 25 da ’yarta Munawwara Sagir ’yar shekara takwas kwance cikin jini male-male.

“Ya sanar mana cewa yana zargin dansa da aikata laifin.

“Bayan samun rahoton faruwar lamarin, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Mamman Dauda, ya umarci CSP Usman Abdullahi da DPO din Rijiyar Zaki da su jagoranci cafke wanda ake zargin.

“Tawagar ‘yan sandan sun garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.”

A cewarsa, an cafke wanda a zargin a wani kango lokacin da yake shiryen-shiryen barin gari.

“Yayin amsa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana yadda shi kadai ya daba wa kishiyar mahaifiyarsa sukundireba a wuya da kuma goshi.

“Sannan ya shake ’yarta har sai da ya tabbata ba ta numfashi, amma ana ci gaba da bincike,” a cewar Kiyawa.