✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe mahaifansa 2 da tabarya a Jigawa

Sai dai ana zargin matashin na da tabin hankali

Wani matashi mai shekara 37 mai suna Munkaila Ahmadu, ya kashe mahaifansa 2 a kauyen Zarada-Sabuwa da ke Karamar Hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa.

A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ’Yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce Munkaila ya yi amfani da tabarya inda ya kaiwa mahaifinsa mai suna Ahmad Muhammad mai shekara 70 hari wanda shi ne Mai Unguwan kauyen da mahaifiyarsa, Hauwa Ahmadu mai shekara 60.

An kuma ruwaito cewa ya kai hari kan wasu mazauna garin da suka hada da Kailu Badugu mai shekara 65 da kuma Hakalima Amadu mai shekara 50.

Ya ce, “Bayan samun wannan mummunan rahoton, jami’an ’yan sanda sun ziyarci inda aka aikata laifin, inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gumel.

“Ahmadu Muhammad da Hauwa Ahmadu likitoci ne suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon raunukan da suka samu a ka, yayin da Kailu Badugu da Hakalima Amadu wadanda suka samu raunuka daban-daban suke jinya a asibitin.”

Kakakin ’yan sandan ya kuma ce an kama wanda ake zargin kuma an gano shaidar aikata laifin a tare da shi.

“Binciken na farko ya nuna cewa, Ahmad Muhammad da Hauwa Ahmadu sun kasance iyayen wanda ake zargin,” inji shi.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Aliyu Sale Tafida, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ke Dutse babban birnin jihar, domin gudanar da bincike na gaskiya tare da gurfanar da mai laifin a gaban kuliya.