✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe mahaifinsa a kan kosan bude-baki

Mutanen Unguwar Gabas da ke garin Kankiya sun yi buda-baki cikin firgici bayan da wani matashi ya kashe mahaifinsa da tabarya sannan ya karya hannun…

Mutanen Unguwar Gabas da ke garin Kankiya sun yi buda-baki cikin firgici bayan da wani matashi ya kashe mahaifinsa da tabarya sannan ya karya hannun mahaifiyarsa don sun hana shi daukar kosan buda-baki saboda ba ya azumi.

Malam Aminu Nasiru makwabcin marigayi Rabe ne da aka fi sani da Aka ya ce, “Mahaifiyar matashin mai suna Lawal, bayan ta farfado ta shaida musu cewa, da misalin karfe 6 na yamma, tana tuyar kosan da za su yi buda-baki, sai Lawal ya shigo ya nufo inda take don dauka ya ci, amma ta hana shi domin ba ya azumi.

Neman dauka da karfi da ya yi, ya sa mahaifinsa ya taso yana yi masa fada. Wannan ya sa Lawal, ya dauko tabarya, ya rika bugun mahaifin da ita.”

Ya ce, ganin haka sai mahaifiyar ta taso don shiga tsakani, inda ya kai mata bugun da tabaryar ya karya mata hannu, ta fadi kasa, ya juya kan mahaifin har sai da ya ga ba ya motsi sannan ya fice daga gidan ya bar su kwance.

Lawal Rabe mai kimanin shekara 27 da ake yi wa lakabi da Mashi, an ce ya gama sakandare, inda ake zargin ya fada shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Wata majiya ta ce, kafin wannan aika-aika, ya taba yi wa wata mahaukaciya fyade aka kai shi gidan gyaran hali amma mahaifinsa Malam Rabe wanda tsohon malamin makaranta ne ya shiga-ya-fita sai da aka fitar da shi.

Bayan jin abin da Lawal ya yi wa mahaifinsa wadansu matasa sun bi shi zuwa inda ya boye suka kamo shi su mika wa ’yan sanda a Kankiya bayan sun yi masa dukan da sai da aka kai shi asibiti.

Washegari Talata da safe ne Malam Rabe ya rasu, yayin da mahaifiyar matashin ke jinyar karayar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za su gurfanar da Lawal Rabe a kotu da zarar sun kammala bincike.