✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya koma karbar jakarsa ta miyagun kwayoyi a hannun ’yan sanda

Yanzu dai da jakar da matashin baki daya suna hannun hukuma.

Wani matashi ya nuna karfin hali inda ya tafi karbo wata jakarsa da ya manta da ita a cikin jirgin kasa a kasar Jamus.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, matashin ya koma karbar jakar a hannun ’yan sanda duk da sanin cewa miyagun kwayoyi ne kunshe a cikinta.

’Yan sandan yankin sun ce, bayan da suka samu sanarwar cigiyar jakar ya sa suka tuntubi matukin jirgin da aka mance da jakar a ciki.

Jami’an sun ce cikin sa’a suka gano jakar tare da sanar da mai ita a kan ya zo ya karbi jakarsa.

Amma kafin nan, binciken ‘yan sandan ya gano haramtattun kwayoyin da ke kunshe cikin jakar wanda hakan ya tabbatar musu matashin mai ta’ammali da miyagun kwayoyi ne.

Ko da matashin ya isa ofishin ‘yan sanda don ya karbi jakarsa, a nan aka yi ram da shi bisa zargin mallakar miyagun kwayoyi.

Yanzu dai da jakar da matashin baki daya suna hannun hukuma don daukar matakin da ya dace.

(NAN)