✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kone kansa saboda ya gaza biyan kudin jarrabawa

Matashin ya yanke kauna da rayuwa yayin da ya bankawa kansa wuta.

Wani matashi mai kimanin shekara 20 a duniya ya banka wa kansa wuta bayan da yunkurinsa na samun kudi domin biyan jarrabawar kammala karatun sakandare (NECO) ya gaza yin nasara.

Lamarin dai ya faru ne a garin Garo da ke Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano ranar Talatar makon da ya gabata.

  1. ‘Ladan N50,000 za a bani na kai dauri 173 na tabar wiwi Daura’
  2. Bidiyon Dala: Kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar N800,000

Rahotanni sun ce sau uku matashin, mai suna Danladi Shu’aibu, yana zana jarrabawar a baya amma ba ya ci, sai kuma a bana da gaba daya ma ya gaza samun kudin da zai biya.

Wani mazaunin garin na Garo, Ya’u Ahmad Garo, ya shaida wa Aminiya cewa da ma matashin ya sha fadar cewa yana jin zai iya kashe kansa matukar bai samu damar rubuta jarrabawar ba, saboda yadda yake matukar son karatu.

Ya’u ya kuma ce bayan ya kama da wuta, an garzaya da matashin asibiti, amma bayan kwana biyu ya ce ga garinku nan.

Kazalika, wata makwabciyar marigayin, wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, “A ranar da abin ya faru, da yake da ma yana zuwa wani gareji yana aiki, da ya samo kudin aikinsa na ranar ashe man fetur ya je ya sayo da su, ya shiga wani daki a gidansu sannan ya banka wa kansa wuta.

Kudin fetur

“Sai da wutar ta ci karfinsa sannan ya fara ihu yana neman taimako.

“A nan ne aka yi nasarar kashe wutar kuma aka kai shi asibiti.

“Amma bayan kwana biyu (ranar Alhamis) sai rai ya yi halinsa sakamakon kunar da ya samu a jikinsa.”

Rahotanni sun kuma ce Danladi ya samu rabin kudin jarrabawar tun da farko, kuma ya yi kokari wajen samo cikon amma bai samu ba, lamarin da ya sa ya yanke kauna.

To sai dai wasu mazauna garin sun ce wani babban dan siyasa a yankin ya yi alkawarin biya wa dukkan daliban da ba su da halin biyan kudin jarrabawar a bana, amma kuma ya gaza cika alkawarin.

Hakan, a cewarsu, ta sa Danladi da ma sauran marasa hali suka gaza biya saboda ko da wani yana da niyyar biya musu in aka ce wancan dan siyaysar ya biya sai ya fasa.