✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya lakada wa mahaifinsa dukan da ya yi ajalinsa

Matashin ya shiga harkar shaye-shaye tun bayan kammala sakandare.

Shaye-shayen miyagun kwayoyi ya sanya wani matashi mai shekara 21 yi wa mahaifinsa dukan kawo wuka, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Matashin da ake zargin ya aikata laifin, shi da mahaifin nasa ne kadai a gida lokacin da lamarin ya faru a unguwar Firamare ta St. Mary a garin Lokoja, a Jihar Kogi.

Wata makwabciyar matashin mai suna Misis Nana Bello, ta ce tun da safiyar ranar Laraba matashin yake nuna wasu halaye na rashin da’a, wanda hakan ta sa shawarci mahaifin da ya yi karar yaron ga jami’an ’yan sanda.

Matashin ya kammala karatun sakandare dinsa, amma ya ki ci gaba da karatu, inda ya bige da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

“Bayan na tashi daga aiki da misalin karfe 10 na dare, na dawo na buga kofa amma babu wanda ya bude.

“Sanin cewa tsohon ba ya fita ko’ina bayan karfe 6 na yamma, hakan ya sa ta tambayi saurayin inda Baba ya tafi.

“Ya amsa daga dakin Baba kuma sanin cewa Baba ba ya barin shi shiga dakinsa, sai na fara shakkar abin da yake yi a dakin kuma nan da nan na kira saurayina,” inji ta.

Ta ce, “Mun kira lambar wayar Baba amma an kashe ta”, inji ta, ta kara da cewa hakan ya sa suka je ofishin ’yan sanda suka kai kara sannan suka dawo gidan tare da ’yan sanda.

“Lokacin da muka shiga dakin, Baba yana kwance cikin jini amma yana numfashi, a haka muka garzaya da shi asibiti. Da safiyar ranar Alhamis ya rasu,” inji Nana.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, DSP Williams Aya, ya ce an cafke wanda ake zargin.

“Mun samu rahoto jiya da misalin karfe 9 na dare cewa wani matashi mai shekara 21 ya raunata mahaifinsa.

“’Yan sanda sun je wurin abin ya faru inda suka riski da wanda lamarin ya faru da shi mai suna usuf Ibrahim a cikin jini a kwance tare da mummunan rauni a kansa.

“An garzaya da shi Asibitin kwararru da ke Lokoja don ba shi agaji, sannan an cafke wanda ake zargin.

“Amma a yau, da misalin karfe 9:30 na safe, daya daga cikin ’ya’yan wanda abin ya rutsa da shi ya ba da rahoton rasuwar mahaifin nasu.

“Don haka, ’yan sanda sun je wurin, suka dauki hotuna suka ajiye gawar a dakin ajiyar gawarwaki don yin bincike”, inji shi.

Ya kara da cewa an fara bincike a kan lamarin.