✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya mutu a rafi a Kano

Matashin ya jima da rasuwa tun kafin zuwan jami'an kashe gobara.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani matashi Ahmad Ali mai shekara 20 da ya nutse a wani rafi da ke garin Larabar Abasawa a Karamar Hukumar Gezawa ta jihar.

Kakakin hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano ranar Talata.

A cewar Abdullahi, hukumar ta samu kiran neman gajin gaggawa a da misalin karfe 1:38 na ranar Litinin daga wani mutum mai suna Isah Abdu.

Ya ce nan take aka tura jami’an hukumar inda suka isa wurin da misalin karfe 1:57 na rana.

Sai dai Abdullahi ya ce tun kafin isar jam’ian matashin ya jima da rasuwa, inda sai gawarsa kawai aka tsamo.

Sannan ya ce an mika gawar matashin ga dan uwansa mai suna Musa Mamuda, inda hukumar ta ci gaba da binciken musababbin mutuwar tasa.