✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya rasu a garin gyaran lantarki a Kano

Daya matashin ya samu mummunan rauni a unguwar Hotoro Tsamiyar Boka.

Wani matashi ya rasu a yayin da yake kokarin tsikarar wutar lantarki domin ta dawo bayan ta dauke a wasu gidaje a unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a Jihar Kano.

Shi ma wani matashi da yake taimaka masa wurin zungurar wutar domin ta dawo a gidajen da ke unguwar ya samu mummunan rauni.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce, “Wani mai suna Abubakar Lawal ya kira mu ta waya da misalin karfe 12:02 na dare.

“Da jin abin da ya faru, da misalin 12:10 sai muka tura masu ceto,” aka garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda likita ya tabbatar da rasuwar mamacin.

Ya bayyana

An ce sunan mamacin Kabiru Muhammad mai shekara 25, sai kuma Sadiq Muhammad mais shekara 17 wanda ya samu rauni.

Ya ce an mika gawar Kabiru ga Baturen ’Yan Sandan Hotoro, ASP Rabiu Hamza, ana kuma ci gaba da bincike kan lamarin.