✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya rasu a yayin ninkaya a kogi a Kano

Wani matashi mai shekara 28 mai suna Rabiu ya rasu a wani rafi da ke Kauyen Gwazaye a Karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano. 

Wani matashi mai shekara 28 mai suna Rabiu ya rasu a wani rafi da ke Kauyen Gwazaye a Karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano. 

Bayanin rasuwar na kunshe cikin wani sako da kakakin  Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar, Saminu Abdullahi, ya rabawa manema labarai a ranar Litinin kan lamarin.

“Mun samu kiran waya daga sashen baturen ’yan sanda sanda mai kula da ayyukan bata-gari da ke unguwar Dorayi Babba, Saifullahi Bello, da misalin karfe 12:27 na rana.

“Nan take muna tura jami’anmu don kai dauki cikin gaggawa da misalin karfe 12:35 na rana zuwa inda lamarin ya faru,’’ inji shi.

Abdullahi ya shaida wa manema labarai cewa an tsamo gawar Rabi’u daga ruwan kuma aka damka shi ga ’yan sanda masu kula da laifuka.

Ya ce, mutumin, lamarin ya ritsa da shi yayin da yake iyo a cikin ruwan sai ruwan ya sha kansa.