✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya sace wayoyin salula 21 na masu zana jarrabawa a Kwara

Ana zargin marashin da tserewa da wayoyin bayan an ba shi ajiyarsu.

Hukumar Sibil Difens (NSCDC) ta cafke wani matashi mai shekara 23 da ake zargi da yin awon gaba da wayoyin salula 21 na daliban da ke rubuta jarrabawar JAMB a Jihar Kwara.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kadiri Qudus a hedikwatar NSCDC da ke Ilorin, kakakin rundunar, Olasunkanmi Ayeni, ya ce matashin ya tsere da wayoyin daliban lokacin da suke tsaka da zana jarrabawar ta neman shiga manyan makarantu.

Ayeni ya ce matashin ya yi basaja a matsayin mai sayar da takunkumin rufe fuska a wata cibiya ta zana jarrabawar wadda Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta gudanar a Ilorin, inda ya karbe wa dalibai wayoyinsu na salula har guda 21 a matsayin ajiya.

Bayanai sun ce wanda ake zargin ya gudu da wayoyinsu gabanin daliban su kammala zana jarrabawar.

Sai dai da yake magana da manema labarai, Qudus ya musanta zargin, inda ya yi ikirarin cewa an sace wayoyin ne daga wurin da ya ajiye su.

“Saboda tsoron abin da zai same ni, ya sa na gudu don tsira da raina,” in ji shi.