✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya shiga hannu kan satar yaro dan makaranta

Matashin ya shiga hannu bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 1.5.

’Yan sanda sun cafke wani matashi kan zargin sace wani yaro mai shekara tara a duniya daga makaranta, don karbar kudin fansa.

Mai magana da yawun hukumar ’yan sandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Frank Mba, ya ce matashin ya dauki yaron daga makaranta inda ya shaida masa cewar iyayensa ne suka turo shi ya dauke shi zuwa makarantar koyon ilimin kwammfuta.

Mba ya ce daga nan matashin ya rike yaron a wajensa har sai da iyayen yaron suka biya shi miliyan N1.5 kudin fansa.

Ya ce an yi nasarar kubutar da yaron sannan an mika shi ga iyayensa, bayan biyan matashin kudin.

Kazalika, ya ce an yi nasarar cafke matashin bayan shigar da kara da iyayen yaron suka yi kan batan dan nasu.