✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya shiga hannu kan zargin aikata fyade a Gombe

Matashin ya amsa laifinsa bayan tuhuma da jami'an 'yan sanda suka yi masa.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi a yankin Tumfure da ke Jihar, kan zargin yi wa wata yarinya fyade.

‘Yan sandan sun cafke matashin da ake zargi a ranar 28 ga watan Fabrairun 2022, bayan shigar da kara da iyayen yarinyar da aka sakaya sunanta suka yi

Kwamishinar ‘yan sandan Jihar, Ishola Babatunde Babaita, ta hannun kakakin ‘yan sandan jihar, SP Mary Obed Malum, ta ce ‘yan sanda sun kama matashin da ake zargi ne da laifin bin yarinyar har gida ya ci zarafinta.

SP Mary ta ce matashi ya bi sahun yarinyar ne inda bayan ya gano gidansu, daga bisani ya tsallaka katangar gidan ya keta mata haddi.

A cewarta, bayan faruwar lamarin ne jami’an sa-kai suka garzaya da yarinyar zuwa asibitin kwararru da ke jihar don duba lafiyarta.

SP Mary ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ta ce nan ba da jimawa ba za a tura shi zuwa kotu don ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata.

Kwamishinar ta ja kuma hankali al’umma musamman masu aikata laifuffuka da cewa su shiga taitayinsu, domin ‘yan sanda suna nan za su ci gaba da zakulo ire-irensu daga cikin al’umma don su gaya wa aya zakinta.