✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya damfari ’yan kasuwar Gombe N40m ya shiga hannu

Za a gurfanar da matashin a gaban kotu da zarar an kammal bincike.

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta ‘Civil Defence’ (NSCDC), sun ka matashi mai shekara 37 da ya damfari wasu ’yan kasuwa 15 kudi sama da Naira miliyan 40 a Jihar Gombe.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga ’yan jarida a hedikwatar hukumar, Kwamandan NSCDC na Jihar Gombe, Waziri Babagoni, ya ce sun samu korafi ne a kan zambar kudin daga wasu da ya damfara, wanda hakan ya sa suka tsare shi don gudanar da bincike.

Babagoni, ya ce matashin ya cuci mutanen kudi sama da Naira miliyan 40, wanda hakan tasa suke karar shi ko kudin su zai fito.

Kwamandan, ya ja hankalin ’yan kasuwa a Jihar Gombe da sauran wurare da su dinga kula da kuma sanin irin mutanen da za su yi huldar kasuwanci da su domin kauce wa fadawa hanun ’yan damfara.

Wasu daga cikin wadanda ya damfara Muhammad Goje, Muhammad Bappah da Salmanu Muhammad, sun shawarci ’yan uwansu ’yan kasuwa da cewa su kasance kodayaushe masu kula da bata-garin mutane macuta ’yan damfara.

Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin wanda ake zargin da ake masa, Kwamandan ya ce da zarar sun kammala bincike a kansa za su gurfanar da shi a gaban kotu.